An yi wa Shugaban kasa martani a kan zuwa Legas, ana makokin mutum 80 a Sokoto

An yi wa Shugaban kasa martani a kan zuwa Legas, ana makokin mutum 80 a Sokoto

  • A yau da safe ne labari ya zo cewa jirgin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura garin Legas
  • Mutane da-dama sun yi ta sukar zuwan Buhari Legas a lokacin da ake jimamin kisan gilla a Sokoto
  • Wasu sun ce wannan abin da shugaban kasar ya yi, ya nuna sam bai damu da mutanen Arewa ba

Nigeria - A yau da safiyar Alhamis, 9 ga watan Disamba, 2021, BBC Hausa ta tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Legas.

Ziyarar da shugaban kasar ya kai Legas bai yi wa mutane da-dama dadi ba, musamman a daidai lokacin da aka ji an hallaka Bayin Allah rututu a Sokoto.

Masu bibiyar shafin Facebook sun rika yin Allah-wadai da wannan ziyara ta shugaban kasar. Kusan da wahala a samu wanda ya fadi wani abin alheri.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad ya tafi hutun Facebook, yace ba zai ce komai ba a halin yanzu domin girmama matafiyan da aka babbaka a hanya.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku wasu daga cikin martanonin da aka bada da jin isar Buhari garin Legas:

Shugaban kasa
Buhari a jirgin sama Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baba Jibril Muhammad ya rubuta:

“Na rantse da Allah ji nake kamar in fashe saboda bakin ciki.. ba don abun da yake Yi Mana yanzu ba, don abinda za'a Yi Mana Nan gaba.”

Bangis Yakawada yana ganin laifin Garba Shehu ne:

“Gaskiya dai wannan cin fuska ne ake yi mana a kaikaice, mutum nawa aka kashe a Lagos da zaku tura shi yaje jaje. Amman ku hana shi ya zo Sokoto inda aka yiwa ƴan uwan sa na jini kisan gilla, wallahi Allah Garba Shehu, se Allah ya tambayeku.”

Kara karanta wannan

Ba zan bar masu hannu a kisan dalibin kwalejin Dowen, Oromoni, su ci bulus ba, Shugaba Buhari

“Su kuma waɗanda aka ƙona a Sokkwoto ba wanda zai je ya yi ta'aziyyarsu kenan? Waɗanda suka kashe su ma ba wanda zai sa a zaƙulo su a yi musu hukunci kenan?” inji Adam Sharada

Al Ameen Arsalan tambaya ya yi, yace “Sokoto fah?”

Sai Abdullahi Adam Abdullahi yam aida masa amsa da cewa: “Buhari ba ya zuwa jaje”

Ahmad Auwal Ahmad ya maida martani: "Allah ya isanmu tsakaninmu da BUHARI & PANTAMI. Allah ya isanmu tsakaninmu da wanda suke ganin dai-dai ake yi a wannan gwamnatin."

An kashe mutane 800 a dare guda

Ku na da labari cewa manyan kasar Sabon Birni sun rubutawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari takarda a kan batun rashin tsaron da ya addabi mutanensu.

Kungiyar Gobir Development Association ta bayyana irin ta’adin da su Bello Turji suke yi na kisa, satar abinci da dukiya, da kuma lalata da matan mutane a kauyuka.

Kara karanta wannan

An ba Bola Tinubu shawarar ya hakura da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel