Sanusi: Gwamnati ta bayyana mataki na gaba bayan tsohon Sarki ya yi nasara a kan ta a kotu

Sanusi: Gwamnati ta bayyana mataki na gaba bayan tsohon Sarki ya yi nasara a kan ta a kotu

  • Kwamishinan shari’a na jihar Kano zai daukaka kara a shari’arsu da Malam Muhammadu Sanusi II
  • Kotu tace kora da tsare tsohon Sarkin da aka yi bayan an cire masa rawani a 2020 ya sabawa doka
  • Babban lauyan gwamnatin Kano, Musa Lawan ya nuna ba su gamsu da hukuncin Anwuli Chikere ba

Kano - Gwamnatin jihar Kano ba ta amince da hukuncin da Alkalin babban kotun tarayya ya zartar a shari’arta da tsohon Sarki, Malam Muhammadu Sanusi II ba.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, 2021 inda ta ce gwamnatin Kano tace dole za ta daukaka wannan kara a kotun gaba.

Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin jihar Kano, Musa Lawan, ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa za su je kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Kotu ta sake sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a zaman shari’ar yau

Mai shari’a Musa Lawan ya sanar da jaridar Solacebase cewa ba su amince da wannan shari’a ba.

Musa Lawan yace dokar kasa ta san da zaman al’ada da tsarin gargajiya da suka bada dama aka tsare Muhammadu Sanusi II a wani kauye a cikin jihar Nasarawa.

Wahalar da gwamnati ta ba Sanusi II

Da aka tunbuke Sanusi a watan Maris 2020, gwamnati ta iza keyarsa zuwa kauyen Loko, daga nan aka tsare shi a wani gida a karamar hukumar Awe, jihar Nasarawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan fitowarsa ne ya tafi Abuja, daga nan ya koma gidansa da ke garin Legas. Tun daga nan tsohon Sarkin bai sake zama a Kano ba, yanzu haka yana kasar Ingila.

Sanusi da Gwamna
Muhammadu Sanusi II da Abdullahi Ganduje Hoto: vanguard da standarddailytimes
Asali: UGC

Da yake kare matakin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka bayan tsige Muhammadu Sanusi II, Mai girma kwamishinan yace ya kamata a kare al’ada.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

Gwamnati ta na ta rashin sa'a a kotu

Da yake bayanin yadda ta kaya a kotu, shahararren 'dan jaridar nan, Jafar Jafar ya rubuta 'What a bad day for Ganduje!', ma'ana ranar ba tayi wa Ganduje kyau ba.

Hakan na zuwa ne bayan kotu ta ba tsagin Ibrahim Shekaau nasara a rikicin APC. Baya ga haka gwamnan Kano ya biya 'dan jaridar N800, 000 da kotu ta bada umarni.

A biya Muhammadu Sanusi N10m - Kotu

Alkali mai shari’a Anwuli Chikere da ta yanke hukunci a makon nan, tace abin da gwamnatin Kano ta yi ya saba doka, kuma an ci zarafi Mai martaba Sanusi II.

Chikere ta bukaci gwamnati ta hannun babban lauyan jihar Kano, jami’an ‘yan sanda da DSS su biya tsohon Sarkin kudi Naira miliyan 10 saboda an ci masa zarafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel