Da Duminsa: Shugaban CPC na farko kuma tsohon na hannun daman Buhari ya fice daga jam'iyyar APC

Da Duminsa: Shugaban CPC na farko kuma tsohon na hannun daman Buhari ya fice daga jam'iyyar APC

  • Tsohon abokin harkar siyasar Buhari kuma fitaccen dan jam’iyyar APC, Sanata Rufai Hanga ya sauya sheka
  • A cewarsa, yanzu APC ba ta da wani tasiri don haka ya yanke shawarar barinta ya kama gabansa
  • Sanata Hanga da babban ginshiki ne mai ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar mai mulki ta APC

Tsohon abokin siyasar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Rufai Hanga ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki a kasa, SaharaReporters ta ruwaito.

Kamar yadda ya shaida, a halin da ake ciki jam’iyyar APC ba ta da wani tasiri don haka bai ga amfanin zama cikinta ba.

Da Duminsa: Shugaban CPC na farko kuma tsohon na hannun daman Buhari ya fice daga jam'iyyar APC
Sanata Rufai Hanga ya fice daga jam'iyyar APC. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Hanga wanda babban ginshiki ne na jam’iyyar, amma yanzu ya duba ya ga babu mamora don haka ya zarga wa karensa igiya.

Kara karanta wannan

APC za ta ɗaɗaice kafin zaɓen shekarar 2023, Gwamna Wike

Har yanzu bai shiga wata jam’iyyar ba

Hanga wanda da shine shugaba jam'iyyar CPC na farko, ya sanar da The Independent cewa har yanzu bai shiga wata jam’iyyar ba.

CPC ce tsohuwar jam’iyyar shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin su yi maja da ACN da sauran jam’iyyu su hada jam’iyyar APC.

A cewar Hanga, duk da ya yi aiki tukuru wurin gina jam’iyyar APC, ba zai zauna yana gani jam’iyyar ta rushe yayin da yake cikinta ba.

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito ya ce:

“Eh duk da na bar jam’iyyar APC, har yanzu ban sanar da jam’iyyar da na koma ba. Amma na bar jam’iyyar kuma ina ganin abubuwan da suke yi yasu-yasu.”

Jonathan: Wasu gwamnonin Arewa sun ji haushi lokacin da na gina wa Almajirai makarantu

Kara karanta wannan

Lokacin mu ne: ‘Dalibin Jami'a mai shekara 28 zai yi takarar Shugaban matasa a Jam’iyyar APC

A wani labarin, Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ce akwai gwamnonin da ba su ji dadin gyaran da ya yi wa makarantun Almajiri ba.

An samu bayanai akan yadda gwamnatin Jonathan ta gina makarantun Almajirai 35 a cikin shekarunsa biyu a lokacin ya na kujerar shugaban kasa, NewsWireNGR ta ruwaito.

Yayin jawabi a taron yaye dalibai a cibiyar ilimin tsaro ta NISS da ke Abuja a ranar Alhamis, Jonathan ya kwatanta Almajirai a matsayin abin da ka iya zama matsala a gaba idan ba a dauki mataki na kula da su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel