Jonathan: Wasu gwamnonin Arewa sun ji haushi lokacin da na gina wa Almajirai makarantu

Jonathan: Wasu gwamnonin Arewa sun ji haushi lokacin da na gina wa Almajirai makarantu

  • An samu bayanai akan yadda gwamnatin Goodluck Jonathan ta gina makarantun almajirai 35 a cikin shekaru biyu lokacin ya na shugaban kasa
  • Yayin jawabi a taron yayen dalibai a cibiyar ilimin tsaro ta tarayya, NISS da ke Abuja a ranar Alhamis, Jonathan ya kwatanta Almajirai a matsayin lokacin bom
  • Ya bukaci gwamnonin jihohin arewa 19 da su kawo gyara akan harkar ilimin almajirai don kawo gyara akan matsalolin tsaron da ke kasar nan

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ce akwai gwamnonin da ba su ji dadin gyaran da ya yi wa makarantun Almajiri ba.

An samu bayanai akan yadda gwamnatin Jonathan ta gina makarantun Almajirai 35 a cikin shekarunsa biyu a lokacin ya na kujerar shugaban kasa, NewsWireNGR ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun kaure da cacar baki kan rashin adalci a daukar ma'aikata a rundunar soji

Yayin jawabi a taron yaye dalibai a cibiyar ilimin tsaro ta NISS da ke Abuja a ranar Alhamis, Jonathan ya kwatanta Almajirai a matsayin abin da ka iya zama matsala a gaba idan ba a dauki mataki na kula da su ba.

Jonathan: Wasu gwamnonin Arewa ba sun ji haushi lokacin da na gina wa Almajirai makarantu
Jonathan ya ce wasu gwamnonin arewa ba su ji dadi ba a lokacin da ya gina wa Almajirai makarantu. Hoto: News Wire NGR
Asali: Facebook

Ya bukaci gwamnonin jihohin arewa 19 da su gyara tsarin ilimin Almajiri don kawo gyara akan rashin tsaron da kasar nan ke fuskanta.

Jonathan ya ce akwai bukatar gwamnoni su zage damtse wurin yin ayyuka

Jonathan ya kara da horar gwamnonin da su aiki tukuru don ba aikin gwamnatin tarayya bane gini da kulawa da makarantu.

Kamar yadda Jonathan ya ce:

“Wata matsalar da ke damunmu ita ce ta rashin tsaro. A Afirka, me yasa muke da matasa marasa ayyukan yi? Akwai yuwuwar rashin aikin yi ne ke kawo ta’addanci.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya karrama wasu 'yan Najeriya 3 'masu gaskiya'

“Hanyoyin shawo kan rashin aikin yi akwai matsalar ilimi. Kamar yadda Nelson Mandela ya ce, idan ka ba mutane ilimi ka ba su makamin sanin abinda ke faruwa a yankinsu.
“Ilimi mabudi ne, don haka idan ba ma da ingantaccen ilimi, dole matsaloli su yi ta barkwewa ta ko ina.”

A cewarsa ilimantar da matasa ce mafita ga matsalar tsaro

Ya kara da cewa idan kasa bata dage wurin bunkasa matasa ba, sai shugabanni sun kashe kudade wurin kulawa da matsalar tsaro.

Akwai hanyoyi da dama da gwamnati za ta bi amma sai gwamnoni sun yi aiki tukuru wurin inganta makarantu don ba aikin gwamnatin tarayya bane, inji tsohon shugaban kasan.

Ya kara da cewa lokacin da ya yi kokarin gyara ilimin almajirai, ta yiwu wasu gwamnonin ba su ji dadi ba, amma ba su sanar da shi hakan ba har sai da ya sauka daga kujerarsa.

Ya ce a lokacinsa anyi amfani da kudin gwamnatin tarayya ta UBE duk don samar da ingantaccen ilimi a jihohi.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya yi wa Jonathan da PDP adawa a kan cire tallafin fetur kafin ya hau mulki

APC za ta ɗaɗaice kafin zaɓen shekarar 2023, Gwamna Wike

A wani labarin, Gwamna Wike na jihar Ribas ya ce akwai yuwuwar jam’iyyar APC ta tarwatse gaba daya sakamakon kalubalen da za ta fuskanta, ba za ta kai labari ba a 2023, The Nation ta ruwaito.

Gwamnan ya alakanta wannan hangen nasan da ya yi akan cewa jam’iyyarsa ta PDP itama zata fuskanci kalubale iri-iri wurin tsayar da dan takarar shugabancin kasa a 2023, amma hakan ba zai girgizata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel