Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari

Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari

  • Kungiyar Agbekoya ta manoma da ke kudancin kasar nan ta yi kira ga Buhari da ya ceci 'yan Najeriya daga yunwa da kuma rashin tsaro
  • Kamar yadda shugaban kungiyar, Kamorudeen Okikiola yace, ya bukaci a sako dan awaren kasar Yarabawa, Chief Sunday Adeyamo
  • Ya ce sun tsaya kan kafarsu wurin bai wa kasar Yarabawa kariya daga 'yan ta'addan Fulani, makiyaya, 'yan bindiga da masu satar mutane

Kungiyar manoma ta Agbekoya da ke Najeriya a jiya ta koka kan yawan yunwa, rashin aikin yi da rashin tsaro da ya addabi kasar nan inda ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauka matakin shawo kansu.

Vanguard ta ruwaito cewa, a yayin jawabi bayan taron majalisar zartarwarsu ta kasa ta kungiyar a Ibadan, shugaban Agbekoya, Chief Kamorudeen Okikiola ya ce ya kamata a dauka mataki domin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari
Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Okikiola, wanda ya bayyana rashin jin dadinsa, ya bukaci a sako dan awaren kasar Yarabawa, Chief Sunday Adeyamo wanda aka fi sani da Sunday Igboho da ke tsare a Cotonou, jamhuriyar Benin.

Ya caccaki cire tallafin man fetur tare da kara farashin litar fetur, hada rundunar tsaron hadin guiwa da ta hada da sojoji, 'yan sanda, jami'an DSS da jami'an NSCDC da kungiyoyi irin su Agbekoya, OPC, mafarauta da 'yan sa kai wurin yaki da rashin tsaro a kudu maso gabas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bukaci a hada kai da masarautun gargajiya tare da taimakon manoma wurin kawo karshen rashin tsaro da yaki da yunwa, Vanguard ta ruwaito.

"Mun shirya bai wa manoma kariya da dukkan kasar Yarabawa komai rintsi da tsanani. Agbekoya ta shirya a koda yaushe wurin kariya da tsare kasar Yarabawa daga Fulani da 'yan ta'addan makiyaya, 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

"Ina son in ja kunnen jami'an tsaro da su guji nuna kabilanci kan yadda suke shawo kan matsalar tsaro a kowanne sassan kasar nan," yace.

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel