2023: Abin da zai hana mu lashe zaben Shugaban kasa da Gwamnonin jihohi inji Jigon PDP

2023: Abin da zai hana mu lashe zaben Shugaban kasa da Gwamnonin jihohi inji Jigon PDP

  • Babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya watau PDP ta na iya cigaba da zaman adawa bayan 2023
  • Umar Sani yace idan PDP ba ta canza halinta ba, to babu mamaki APC ta sake yin galaba a kanta
  • Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana matsalolin da suke damun jam’iyyar PDP

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ba ta da tabbacin karbe mulki a jihohi da gwamnatin tarayya a zabe mai zuwa na 2023, a cewar Alhaji Umar Sani.

Daily Trust ta rahoto Umar Sani yana wannan bayani a wajen wani taron manema labarai da aka shirya a Abuja, a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2021.

Sani wanda shi ne mai ba tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo shawara a kan harkokin yada labarai yace PDP na fuskantar kalubale.

Kara karanta wannan

2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari

A cewar ‘dan siyasar, jam’iyyar PDP mai hamayya ta gamu da sabani a kusan kowane mataki, wanda hakan ya jawo mata rabuwar kai a jihar Kaduna.

Yadda PDP ta barke a Kaduna

A halin yanzu akwai bangarenAhmad Makarfi, da bangaren mai gidan Umar Sani watau Namadi Sambo da kuma wasu ‘yan tafiyar Restoration movement.

Zaben Shugaban kasa
Atiku ya na kamfe a Kaduna Hoto: africaprimenews.com
Asali: UGC

Jaridar ta rahoto Sani yana cewa a sama, gwamnonin jihohi sun yi kabe-kabe, har sun yi sanadiyyar korar shugaban jam’iyya, Prince Uche Secondus.

“Idan Uche Secondus ya yi nasara a kotu, hakan ya na nufin shugabannin jam’iyyar da aka zaba sun tashi aiki, kuma hakan matsala ne ga shirin 2023.”
“Muddin jam’iyyar PDP ba ta daina kama-karyarta ba, ta sasanta cikin gidanta, hakan zai yi tasiri wajen gaza komawanta kan mulki.” - Umar Sani.

Kara karanta wannan

Rigima ta nemi ta kaure a taron Gwamnonin APC, sai da Shugaban Gwamnoni ya tsoma baki

Rashin tsaro a Najeriya

A zantawar da ya yi da ‘yan jarida a birnin tarayya Abuja, Sani wanda da su aka kafa jam’iyyar ta PDP a 1998 ya koka a kan matsalar tsaro da ake fama da ita.

Alhaji Sani ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar nan.

Abba gida gida v Ganduje

Kwanan nan wani Jagoran APC a Kano, Nura Hussaini Ungogo ya fallasa yadda aka murde zaben 2019 domin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zarce a 2019.

Nura Hussaini Ungogo ya fito ya shaidawa Duniya yadda APC ta koma mulki, inda yace da zaben gaskiya aka ayi, da tuni Abba Kabiru Yusuf ne gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel