Gaba da gaban ta: Bidiyo da hotunan Tinubu ya na jinjina, gurfane gaban Aminu Dantata

Gaba da gaban ta: Bidiyo da hotunan Tinubu ya na jinjina, gurfane gaban Aminu Dantata

  • Bola Ahmed Tinubu dan siyasa ne da ya san darajar furfura da kuma dattako a rayuwa, ballatana a tsarin al'adar Afrika
  • Jigon jam'iyya mai mulkin ta APC bai yi wasa ba wurin gurfana ya gaida fitaccen dan kasuwan Kano, Alhaji Aminu Dantata
  • Tinubu da wasu jiga-jigan 'yan siyasa sun kai wa Dantata ziyarar ta'aziyya a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba na rasuwar Sani Dangote

Kano - Bidiyon yadda Asiwaju Ahmed Bola Tinubu da wasu 'yan siyasa suna gaida fitaccen dan kasuwan Kano, Alhaji Aminu Dantata yayin da suka ziyarcesa a Kano ya bayyana.

Jigon jam'iyyar APCn an gan shi ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba ya na gaida Dantata cike da mutuntawa da ganin girma.

Gaba da gaban ta: Bidiyo da hotunan Tinubu ya na jinjina, gurfane gaban Aminu Dantata
Gaba da gaban ta: Bidiyo da hotunan Tinubu ya na jinjina, gurfane gaban Aminu Dantata. Hoto daga Abubakar Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Duk a cikin mutuntawa da girmamawa, sauran mutanen da ke falon sun kasa mika wa Dantata hannu domin gaisawa kamar yadda Tinubu yayi. Sai dai dan siyasan ya durkusar da kan shi tare da rike hannayensa biyu a hade.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

Hakazalika, irin wannan girmamawar ce aka ga gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Mawallafin Ovation magazine, wanda a halin yanzu dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne, Dele Momodu, ya kwantanta wannan lokacin da:

"Hakan ne ake gane asalin ubangidan. Ya shigo amma gwamnoni sun mike. Hatta Tinubu ya sadda kai. Wannan shi ne Dantata.
"Kai! Duba irin karfin ikon da mutumin nan ke da shi a nan. Ya mika musu hannu, amma sun kasa bayar da nasu saboda mutunta mai kudin da suke yi.
"Wannan mutuncin ya yi yawa. Karfin iko, wannan shi ne ake kira da karfin iko. Dukkan jama'ar dakin sun tashi tsaye. Idan ka na da girma, ka na da girma kawai. Akwai matakin komai..."

Ga bidiyon da Daily Trust ta wallafa:

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja

Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote

A wani labarina daban, jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya ziyarci jihar Kano a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba.

Tinubu ya ziyarci jihar Kano ne domin gaisuwar ta'aziyya ga mai kudin Afrika, Aliko Dangote, kan rashi da yayi na kaninsa.

Tinubu ya samu tarba daga gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, mataimakinsa, Nasir Gawuna da sauran manyan yan siyasar jihar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, jaridar Independent ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel