Shugaban kasa a 2023: Tinubu ya yi ganawar sirri da Orji Kalu a Abuja

Shugaban kasa a 2023: Tinubu ya yi ganawar sirri da Orji Kalu a Abuja

  • Babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya shiga labule tare da tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, a Abuja
  • Shugabannin biyu sun yi ganawar ne a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba a gidan Kalu
  • Ana zaton ganawar tasu ba zata rasa nasaba da hada-hadar siyasa kan wanda zai gaji shugaba Buhari a 2023 ba

Abuja - Jagoran jam’iyyar All Progessives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, na cikin wata ganawa da tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, a Abuja.

Jaridar Punch ta rahotio cewa Tinubu ya isa gidan Kalu da karfe 4:25 na yammacin yau Asabar, 20 ga watan Nuwamba.

Shugaban kasa a 2023: Tinubu ya yi ganawar sirri da Orji Kalu a Abuja
Shugaban kasa a 2023: Tinubu ya yi ganawar sirri da Orji Kalu a Abuja Hoto: Progressives for Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yan siyasar sun rungume junansu tare da yin gaishe-gaishe a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

An tattaro cewa bayan gaisawar sai suka shiga cikin ganawar sirri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta yi bayanin cewa kafin ganawar sirrin, Kalu ya yi godiya ga Allah a kan warkwar Tinubu cikin sauri.

Tinubu ya dawo Najeriya a ranar 8 ga watan Oktoba, bayan ya shafe wasu watanni a Landan, inda aka yi masa aiki a gwiwa.

Zuwa yanzu ba a san dalilin ganawar tasu ba amma ana ganin ba zai rasa nasaba da wasu ci gaba na siyasa da tattalin arziki a kasar ba.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin shugabannin biyu na hararar kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Su dukkaninsu sun kasance tsoffin gwamnonin jihohinsu daga 1999 zuwa 2007.

2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari

A wani labarin, mun ji cewa akalla sarakunan gargajiya sama da 300 daga kudu maso yamma ne ke goyon bayan takarar tsohon gwamnan jihar Lagas, Sanata Bola Tinubu, a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

Sanata Dayo Adeyeye, shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu ne ya bayyana hakan a Gbongan, jihar Osun, rahoton Punch.

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kungiyar mai suna ‘South West Agenda for Asiwaju for 2023’ a mazabar Irewole.

Asali: Legit.ng

Online view pixel