Rahoton EndSARS: Dan majalisa na PDP ya nemi Buhari ya tsige Lai Mohammed

Rahoton EndSARS: Dan majalisa na PDP ya nemi Buhari ya tsige Lai Mohammed

  • Ana ci gaba da kiraye-kiraye ga Buhari kan ya tsige ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed idan har ya ki yin murabus da kansa
  • Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Ndudi Elumelu ya shiga sahun masu wannan kira
  • Ana dai zargin Lai da yi wa al'umman kasar karya kan lamarin kisan gillar da aka yi wa matasa a Lekki Toll gate a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020

Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai ya bukaci ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed da ya gaggauta yin murabus ko kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallame shi.

Kiran da dan majalisar yayi martani ne ga sharhin da Mohammed yayi a baya kan kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki Toll Gate a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020, kafin kwamitin binciken lamarin ya saki rahotonsa.

Kara karanta wannan

Jagoran APC a Neja ya shawarci Buhari da ya tsige Lai Mohammed daga kujerar minista

Rahoton EndSARS: Dan majalisa na PDP ya nemi Buhari ya tsige Lai Mohammed
Rahoton EndSARS: Dan majalisa na PDP ya nemi Buhari ya tsige Lai Mohammed Hoto: Punch
Asali: Twitter

Rahoton kwamitin ya bayyana lamarin a matsayin kisan gilla sabanin matsayar Lai Mohammed na baya.

Ndudi Elumelu ya gabatar da bukatarsa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba mai taken 'Rahoton EndSARS na Lagas: Jami'an gwamnatin tarayya na da tambayoyin amsawa - Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai'.

Sanarwar ta ce:

"Tabbatarwar da kwamitin Lagas ta yi cewa lallai an yi kisan gilla a Lekki Toll Gate a yayin zanga-zangar EndSARS na 2020 a Lagas da kuma cewa jami’an tsaron da ke karkashin gwamnatin APC sun kwashe gawarwaki tare da tattara shaidu, ya dora wa Gwamnatin Tarayya wacce ta karyata kisan nauyi sosai.
"Saboda haka, shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai yana mamakin dalilin da yasa ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya san gaskiya, gaggawan fitowa a kafofin watsa labarai kafin kwamitin bincike, don cewa lallai ba a kashe kowa ba a Lekki Tollgate, duk da shaidun da wadanda abun ya faru a idanunsu suka bayar.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

“Duk da cewa kowa ya san irin karyar da gwamnatin APC ke yi wa ‘yan Najeriya a kan al’amura, kungiyarmu ta yi mamakin yadda gwamnati za ta iya yin karya kan lamarin da ke da alaka da kisan gilla da ake yi wa ‘yan kasa, musamman matasanmu sannan har ma da yunkurin bayar da kariya ga masu laifin."

A cewarsa, rahoton kwamitin binciken lamarin ya nuna cewa duk daren dadewa, karya fure take bata 'ya'ya.

'Yan majalisar sun bayyana cewa jinin bayin Allah da aka kashe a Lekki Tollgate na neman adalci kuma makasansu da wadanda suka mara masu baya ko yi masu rufa-rufa ba za su taba samun sukuni ba.

“Saboda haka marasa rinjaye, suna kira ga gwamnatin APC da ta fito ta wanke kanta da yin watsi da rufa-rufan da ake kokarin yi kan kashe-kashen.
“Haka zalika, idan aka yi la’akari da sakamakon binciken kwamitin Legas, ana sa ran ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, zai yi murabus nan take ko kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kore shi."

Kara karanta wannan

Abubuwa 17 da ya kamata ku sani a rahoton da kwamitin Endsars ya gabatar

Jagoran APC a Neja ya shawarci Buhari da ya tsige Lai Mohammed daga kujerar minista

A gefe guda, tsohon kwamishinan labarai kuma jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya yi kira ga ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed da yayi murabus.

Vatsa ya kuma bukaci ministan labaran da ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan cewa da yayi babu wanda aka kashe a lokacin harbin toll gate, jaridar The Sun ta rahoto.

Har ila yau jigon na APC ya bayyana cewa ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige ministan nasa idan har ya ki yin murabus da hannunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel