2023: Jagoran APC Bola Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan mutum 50,000 a wannan jiha

2023: Jagoran APC Bola Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan mutum 50,000 a wannan jiha

  • Shugabannin APC na shirin haɗa wa jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, mambobin APC 50,000 a jihar Ribas
  • A cewar tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Okocha, zasu tabbatar da mara wa Tinubu baya har zuwa ya zama shugaban ƙasa
  • Okocha ya yaba wa majalisun tarayya bisa matakin da suka ɗauka na amince wa da zaɓen fidda gwani kai tsaye ga jam'iyyun siyasa

Rivers - Tsohon shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jihar Ribas, Chief Tony Okocha, yace shugabannin APC a jihar sun fara shirin haɗa mambobi 50,000 domin goyon bayan Tinubu.

Leadership ta rahoto cewa zasu haɗa waɗan nan mutanen ne domin nuna goyon bayansu ga jagoran APC, Bola Tinubu, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2023: Mika shugabancin Najeriya ga Igbo zai kawo karshen fafutukar IPOB, Ohanaeze, MBF

Okocha, wanda ya rike mukamin shugaban ma'aikata lokacin mulkin tsohon gwamna, Rotimi Amaechi, ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai a Patakwal.

Bola Tinubu
Takarar shugaban kasa a 2023: Jagoran APC Bola Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan mutum 50,000 a wannan jiha Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya APC ke ganin zaɓen yan tike?

Ya kuma yaba wa majalisun tarayyan Najeriya bisa matakin da suka ɗauka na gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye ga jam'iyyun siyasa.

A cewarsa da wannan matakin kaɗai, yan majalisun tarayya sun ɗauki karfin ikon fidda gwani sun mika wa al'umma, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jigon APC yace:

"Muna godiya ga majalisun ƙasa bisa amince wa da maida karfin iko hannun mutane. Bisa matakin da suka ɗauka na fitad da gwani kai tsaye, sun baiwa mutane damar su."
"Muna nan muna shirya wa takarar Bola Tinubu, kuma fatan mu shine mu haɗa mambobin APC 50,000 a jihar Ribas kaɗai."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Har yanzun fusunoni 3,906 sun yi batan dabo tun bayan hare-haren gidan gyaran hali

"Domin muna son taka rawar gani wajen zaben fitar da ɗan takara, ya samu tikiti kuma mu zaɓe shi ya zama shugaban ƙasar Najeriya.

Shin Tinubu ya dace da zama shugaban kasa?

Okocha, wanda shine shugaban ƙungiyar dake goyon bayan takarar Tinubu,(BATSV) a jihar Ribas, ya bayyana gwanin nasa a matsayin wanda ya dace kuma yake da kwarewar zama shugaba.

A wani labarin kuma Jerin matakan da zaka bi, ka mallaki gida a saukake a shirin cefanar da gidaje na FG

A ranar Jumu'a 12 ga watan Nuwamba, Gwamnatin tarayya ta sanar da bude shafin intanet domin siyar da gidaje ga yan Najeriya.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yace jihohi 34 da babban birnin tarayya Abuja zasu samu damar shiga shafin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel