Da Dumi-Dumi: Har yanzun fusunoni 3,906 sun yi batan dabo tun bayan hare-haren gidan gyaran hali, Minista

Da Dumi-Dumi: Har yanzun fusunoni 3,906 sun yi batan dabo tun bayan hare-haren gidan gyaran hali, Minista

  • Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, yace tun daga shekarar 2020 zuwa yanzun fursuna 4,369 ne suka tsere
  • A cewarsa jami'ai sun sake damke mutum 984 yayin da har yanzun ake neman mutum 3,906
  • Ministan yace akwai yan gidan gyaran hali dake karatun digirin farko, na biyu, har ma da digiri na uku a fannoni daban-daban

Abuja - Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, yace har yanzun ba'a san inda fursunoni 3,906 suke ba, tun bayan harin gidan gyaran hali daban-daban a faɗin Najeriya.

Dailytrust tace Ministan ya faɗi haka ne ranar Alhamis, yayin taron manema labarai da aka shirya a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Minsitan ya bayyana cewa fursunoni 4,369 ne suka tsere da gidan gyaran hali daban-daban tun daga shekarar 2020 zuwa yanzun.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2021: Shugaba Buhari na da hakuri wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Najeriya, Dan majalisa

Rauf Aregbesola
Da Dumi-Dumi: Har yanzun fusunoni 3,906 sun yi batan dabo tun bayan hare-haren gidan gyaran hali, Minista Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya kuma ƙara da cewa tun wannan lokaci an samu nasarar sake cafke guda 984 kacal tare da maida su gidan yari.

Wane mataki gwamnati ke ɗauka?

Ministan yace gwamnati na da shaidar bayanan yatsu na kowane fursuna dake faɗin gidajen gyaran hali a ƙasar nan.

A cewarsa hakan zai taimaka wajen gano waɗan da suka tsere, yayin da jami'ai ke cigaba da aiki kafaɗa-kafaɗa da yan sandan ƙasa da ƙasa domin sake damke su.

The Nation ta ruwaito Ministan yace:

"Tsawon wane lokaci zaku ɗauka kuna gudu a cikin ƙasa? Gwamnati tana da hakuri, zaku iya guduwa amma ba zaku iya ɓoyewa ba."
"Muna da shaidar zanen ku, duk inda kuka je, kuka shiga wata harkalla ta kasuwanci, nan take za'a gano ku."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

Fursunoni na karatun boko

Ministan ya kuma tabbatar da cewa akwai yan gidan gyaran hali mutum 465 dake karatun digirin su na farko a fannoni daban-daban a faɗin ƙasa.

Daga cikin su akwai mutum 85 dake karatun digirin su na biyu, wanda ya haɗa da mutum 4 dake karatun digiri na uku, a cewar ministan.

Hakanan kuma yace an saka fursunoni 560 su zana jarabawar kammala sakandire WAEC/NECO, yayin da wasu 2,300 suka fara karatun yaƙi da jahilci.

A wani labarin na daban kuma Dan majalisar dokokin jihar Legas, Jude Idimogu, yace shugaba Buhari na da hakuri wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Najeriya

A cewarsa sakamakon zaɓen Edo da Ondo, da kuma na kwanan nan a Anambra ya nuna alamun samun cigaba a tsarin zaɓen ƙasar nan.

Ya kuma ya ba wa shugaban bisa yadda gwamnatinsa ta tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2021: Akwai sauran rina a kaba, inji dan takarar PDP, Valentine

Asali: Legit.ng

Online view pixel