Bidiyon yadda sojoji suka ladabtar da wani mutum da ya karya dokar hanya a Abuja

Bidiyon yadda sojoji suka ladabtar da wani mutum da ya karya dokar hanya a Abuja

  • Wani mutumi ya hadu da gamonsa bayan ya karya ka'idar tuki a yankin Apo da ke babbar birnin tarayya Abuja
  • Sojoji ne suka damke mutumin inda suka ladabtar da shi ta hanyarsa sanya shi hawa saman motarsa
  • Mutane da dama sun tofa albarkacin bakunansu a kan wannan hukunci mai ban al'ajabi da aka yankewa direban

Abuja - Jama'a sun tofa albarkacin bakunan bayan bayyanar bidiyon wani mutumi da sojoji suka hukunta sakamakon karya dokar tuki da ya yi a yankin Apo da ke babbar birnin tarayya Abuja.

Shafin @instablog9ja ne ya wallafa bidiyon a Instagram. An kuma tattaro cewa direban ya fita ne daga layinsa zuwa wani sai kawai jami'an tsaron suka yi ram da shi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan shafe kusan watanni hudu a hannunsu, yan Boko Haram sun saki ma'aikacin gwamnatin Yobe

Bidiyon yadda sojoji suka hukunta wani mutum da ya karya dokar hanya a Abuja
Bidiyon yadda sojoji suka hukunta wani mutum da ya karya dokar hanya a Abuja Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Hukuncin da suka yanke masa shine ya dare saman motarsa sannan ya dunga gaishe da mutanen da ke wucewa ta hanyar daga masu hannu.

Kalli bidiyon wanda tuni yayi fice a yanar gizo:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama'a sun yi martani a kan bidiyon

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane suka yi a kan wannan hukunci mai ban al'ajabi da aka yanke wa direban.

dee_billionaire ya yi martani:

"A ko wani yanayi sojoji na iya sanya mutum ya zama mai kankan da kai "

azze_rugsandcarpet ya ce:

" ya dai fi shan duka"

oba_823 ya ce:

"A kalla dai basu yi masa duka ko kashe shi ba. HMMM Najeriya wani wuri ne mai wuyar zama a yanzu! "

l_a_w_a__l ya ce:

"Najeriya sun san yadda ake amfani da mutum fa "

Kara karanta wannan

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

chu6x ya ce:

"Hukuncin sojoji na daban ne...Ban san yadda ake yi suke samun kundin hukuncinsu ba."

Da ina da iko, da na wajabtawa maza auren mata biyu – Jami’ar bincike

A wani labari na daban, wata jami'ar bincike ta bayyana cewa da ace tana da iko, toh da za ta wajabtawa maza auren mata biyu domin rage yawan zinace-zinace da lalata.

A cewar matar 'yar kasar Kenyan, Jame Mugo, dabi'ar magidanta na yin lalata da yan mata a wajen gidajen aurensu na karuwa a kullun.

Ta rubuta a shafinta na Instagram:

"Da ace ina da iko, da na tilastawa maza auren mata biyu. Wasu mazan na amfani da mata, kananan yara domin samun arziki, zamantakewa da nutsuwar zuciya sannan daga baya su watsar da su."

Asali: Legit.ng

Online view pixel