Yayin da Buhari baya nan, Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC ta kasa, Mala Buni ya shiga tasku

Yayin da Buhari baya nan, Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC ta kasa, Mala Buni ya shiga tasku

  • Sabon rikici ya barke a cikin jam'iyyar APC mai mulki inda aka fara kiran kwamitin rikon kwarya ya aje aikinsa
  • Masu ruwa da tsaki na APC ta ƙasa sun bayyana cewa kwamitin da Mala Buni ke jagoranta ya ƙara kassara APC ne mai makon gyara ta
  • A cewarsu kwamitin ne sanadiyyar kayen da APC ta sha a zaben gwamnan jihar Anambra

Abuja - Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a APC sun bukaci kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni, ya aje aikinsa ko su yi fatali da shi.

Da yake jawabi ga manema labarai ranar Alhamis a Abuja, kakakin kwamitin masu ruwa da tsaki, Mista Ayo Oyalowo, yace kwamitin Buni ya gaza shawo kan rikicin da yaƙi ci yaƙi cinyewa a APC.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Buni, Peter Obi, Uzodinma da manyan mutane 4 da APGA ta tonawa asiri

Ya kuma yi zargin cewa kwamitin ba shi na wani shiri na shirya babban gangamin taron jam'iyyar APC na ƙasa nan ƙusa, kamar yadda dailytrust ta rahoto.

Jam'iyyar APC
Yayin da Buhari baya nan, Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC ta kasa, Mala Buni ya shiga tasku Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Hakanan kuma ya kira tarukan APC a matakin gundumomi, ƙananan hukumomi da jihohi a matsayin mafi muni.

Mista Oyalowo yace tarukan da Kwmaitin ya gudanar, maimakon ya kara wa jam'iyyar ƙarfi, sai ya koma yana raba kan mambobin jam'iyya.

Dalilin da yasa APC ta sha ƙasa a Anambra

Oyalowo yace:

"Gazawar kwamitin Buni ne ya jawo rashin nasarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan Anambra na ranar 6 ga watan Nuwamba. Kuma an samu matsala ne tun a zaɓen fidda gwani."

Ya ƙara da cewa tun farko sun tura sako ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, mataimakinsa, Yemi Osinbajo, jagoran APC Bola Tinubu, Sanata Ahmad Lawan da Kakakin majalisa Femi Gbajabiamila, domin su shiga ciki.

Kara karanta wannan

Shugabannin APC na shirin tsayar da gwamnan Arewa takarar shugaban ƙasa a 2023

Oyalowo, wanda ya wakilci wasu mambobin kwamitinsu, ya kuma nuna goyon bayansa kan tsarin fitar da ɗan takara kai tsaye a zaɓen ƙasar nan.

"Sanannen abu ne ga dukkan mambobin APC maza da mata cewa kwamitin rikon kwarya ba zai iya shawo kan matsalolin da ake fama da su ba."
"Kwamitin ya haifar da wasu matsalolin maimakon ya warware waɗan da ya samu a jam'iyya."

A wani labarin kuma dan majalisar dokoki ya jinjina wa shugaban ƙasa Buhari bisa namijin kokarinsa wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Najeriya

A cewarsa sakamakon zaɓen Edo da Ondo, da kuma na kwanan nanɓa Anambra ya nuna alamun samun cigaba a tsarin zaɓen ƙasar nan.

Ya kuma ya ba wa shugaban bisa yadda gwamnatinsa ta tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel