Shugabannin APC na shirin tsayar da gwamnan Arewa takarar shugaban ƙasa a 2023

Shugabannin APC na shirin tsayar da gwamnan Arewa takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Shugabannin jam'iyyar APC na jihar Filato sun fara shirin kaddamar da takarar gwamna Lalong a babban zaɓen 2023
  • A cewarsu gwamnan yana da kwarewar siyasa wajen ɗaukaka darajar Najeriya zuwa gaba idan ya zama shugabn ƙasa
  • Sun kuma bayyana cewa da sun kammala tattaunawa da kowane yanki zasu bayyana aniyarsu a fili

Plateau - Shugabannin APC na jihar Filato sun kare kudirinsu na mara wa gwamna Lalong baya ya nemi kujera lamba ɗaya a Najeriya a zaɓen 2023 dake tafe.

Dailytrust tace Yayin gawarsu a Jos ranar Lahadi domin tattauna kudirin mara wa Lalonga baya, Shugabannin sun kuma tattauna kan rikicin dake wakana a majalisar dokokin jihar.

A taron nasu, shugabannin sun bayyana cewa Lalong yasan hanyoyin shawo kan matsalolin siyasa, hakan yasa rikicin majisar bai yi muni ba.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin gini mai hawa 21 da yan uwansa kan gadon kudaɗe da motocin alfarma

Simon Lalong
Shugabannin APC na shirin tsayar da gwamnan Arewa takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Meyasa suke son gwamnan ya nemi takara a 2023?

Da yake zantawa da manema labarai a madadin shugabannin jim kaɗan bayan taronsu, Saleh Mandung Zazzaga, yace gwamna Lalong zai ɗaga martabar ƙasar nan zuwa inda mutane basa tsammani.

A cewarsa sun yi wannan hasashen ne duba da nasarorin da ya samu na rikice-rikice da kuma yadda ya saita sabanin da ake samu na ƙabila ko addini a jihar Filato, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa duk da rikicin da ake samu nan da can, gwamnan bai yi ƙasa a guiwa ba wajen jawo kowane bangare a cikin gwamnatinsa.

Yace:

"Lalong ne yake jagorantar ƙungiyar gwamnonin Arewa, kuma mafi yawan mutanen wannan yanki da ma na waje na yaba wa da tsarin mulkinsa."

Kara karanta wannan

Tsumagiyar Kan Hanya: Barayin da suka sace masu ibada 60 a Kaduna sun bukaci buhunan shinkafa da jarkokin mai

Lalong yana da kwarewar da Najeriya ke bukata

Zazzaga ya kara da cewa gwamna Lalong yana da duk wata kwarewar siyasa wajen ɗaukaka Najeriya zuwa babban matsayi da kuma ƙara dankon haɗin kai.

Daga ƙarshe yace sun kammala shirin mara wa takarar gwmanan baya a 2023 kuma ba da jimawa ba zasu kaddamar da ita, amma a yanzun suna tattaunawar neman shawara ne daga kowane sashin ƙasar nan.

A wani labarin kuma Gwamnan APC ya rushe shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

Gwamnan Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya sallami ciyamomi 21 da kuma kansiloli dake faɗin jiharsa.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis, gwamnan ya gode wa ciyamomin bisa aikin da suka yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel