Guguwar sauya sheka: Mambobin jam'iyyar PDP Mata sama da 3,000 sun koma jam'iyyar APC a jihar Arewa

Guguwar sauya sheka: Mambobin jam'iyyar PDP Mata sama da 3,000 sun koma jam'iyyar APC a jihar Arewa

  • Tawagar mata yan siyasa mambobin PDP sama da 3,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kwara
  • A cewar matan sun ɗauki wannan mataki ne saboda muhimmancin da gwamnan jihar ya ke baiwa mata wajen tafiyar da mulkinsa
  • Shugabar mata a jam'iyyar APC reshen Kwara, Falilat Muhammed, ta yaba wa mata bisa goyon bayansu ga gwamna

Kwara - Mata sama da 3,000 yan jam'iyyar hamayya PDP, sun koma jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kwara, ranar Laraba.

Tribune Online ta ruwaito cewa matan da suka sauya shekan sun fito ne daga gundumar Ibagun a ƙaramar hukumar Ilorin ta gabas.

A cewarsu, jawo mata a cikin gwamnatin gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq musamman bayyana Hajiya Falilat Mohammed a matsayin shugaban mata ta jam'iyyar APC, sune suka ja hankalinsu.

Read also

Da Dumi-Dumi: Dan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar hamayya, ya koma APC mai mulki

Guguwar sauya sheka
Guguwar sauya sheka: Mambobin jam'iyyar PDP Mata sama da 3,000 sun koma jam'iyyar APC a jihar Arewa Hoto: tribuneonlineng.com
Source: UGC

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, shine ya karbi matan da suka sauya shekan, bisa wakilcin mai ba shi shawara kan siyasa, Alhaji Abdullateef, da kuma shugaban APC na jiha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa matan suka koma APC?

Da take jawabi a madadin tawagar masu sauya sheka, Hajiya Balikis Abdurauf, tace yadda gwamna ke baiwa mata muhimmanci a gwamnatinsa ne ya basu ƙarfin guiwar komawa APC.

Ta kuma bayyana wasu shirye-shirye na dogaro da kai da gwamnatin jiha ta aiwatar wa mata cikin shekaru biyu, da kuma naɗa mata a wasu mukaman gwamnati.

Ta ƙara da ikirarin cewa gwamnatin kwara ta fi kowace gwamnati saka mata a majalisar zartarwa a fadin Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Daga nan kuma matan sun nuna tsantsar goyon bayan su ga gwamnan, tare da kira gare shi ya nemi tazarce a shekarar 2023.

Read also

Matashi dan shekara 36 daga arewa yana neman 'kujera ta daya' a APC

Gwamnati ta tallafawa mata 10,000

Shugabar mata ta APC a jihar Kwara, Hajiya Falilat Mohammed, ta gode wa masu sauya shekan bisa ɗumbin goyon bayan da suke baiwa gwamna.

Tace:

"Mata sama da 10,000 a gudumar Ibagun suka amfana da shirin dogaro da kai na gwamnatin jihar Kwara a lokuta daban-daban."

A wani labarin na daban kuma wani Dan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar hamayya, ya koma APC mai mulki

Jam'iyyar APC mai mulki ta yi babban kamu a majalisar dokoki, inda wani ɗan majalisa ya sauya sheka zuwa APC.

Kakakin majaisar wakilai, Femi Gbajabiamila , shine ya sanar da sauya shekar Ajao Adejumo, daga ADP zuwa APC.

Source: Legit.ng

Online view pixel