Matashi dan shekara 36 daga arewa yana neman 'kujera ta daya' a APC

Matashi dan shekara 36 daga arewa yana neman 'kujera ta daya' a APC

  • Mohammed Saidu Etsu ya bayyana aniyarsa na son tsayawa takarar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa
  • Matashin mai shekaru 36 ya ce ya yanke shawarar ne sakamakon hukuncin da jam'iyyar ta yanke na ba matasa damar shiga a fafata da su a shugabancin jam'iyyar
  • Etsu ya kasance hadimin gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello

Neja - Wani hadimin gwamnan jihar Neja mai shekaru 36, Mohammed Saidu Etsu, ya nuna ra'ayinsa na takarar kujerar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.

The Cable ta rahoto cewa Etsu ya nuna muradinsa na takarar kujerar ne a cikin wani wasika mai kwanan wata 4 ga Nuwamba sannan ya aike shi zuwa ga gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello.

Matashi dan shekara 36 daga arewa yana neman kujera ta daya a APC
Matashi dan shekara 36 daga arewa yana neman kujera ta daya a APC Hoto: Mohammed Saidu Etsu
Asali: Facebook

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa yana son takarar kujerar ne biyo bayan hukuncin jam'iyyar na karfafa wa matasa gwiwar neman mukaman shugabanci, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan Yobe zai gana da wasu jiga-jigan APC don dinke barakar APC a jihar Oyo

Ya ce:

"Sunana Mohammed Saidu Etsu, shekaruna 36, dan asalin jihar Neja kuma babban mai ba gwamnan jihar Neja shawara kan ayyukan samar da wutar lantarki a yankunan karkara kuma dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
"Don haka ina rubutu game da batun da ke sama. Sakamakon shawarar da jam’iyyar ta yanke na karfafa wa matasa gwiwar neman mukaman shugabanci da kuma burina na son a fafata da ni a matakin sama na jam'iyyar, na yi niyyar tsayawa takarar shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa a babban taro mai zuwa.
“Sakamakon abubuwan da ke sama, akwai bukatar zaburar da matasan yankunan kasar guda shida don su marawa kudirina baya wanda za a aiwatar a karkashin kungiyar yakin neman zabena (APC Reset Agenda).
"Ya mai girma, duba ga matsayinka na shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC a arewa ta tsakiya kuma shugaban jam'iyyar na daya a jihar, ina neman goyon bayanka a wannan kudiri nawa domin hakan zai taimaka matuka wajen samun goyon bayan matasa a yankinka.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan arewa sun nuna goyon bayansu ga shahararren dan siyasar kudu

Etsu ya ce ya rike mukamin shugaban matasan jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) a karamar hukumar Edati ta jihar Neja.

Ya kuma kasance mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 da 2019.

Dan takarar da ka iya zama shugaban APC na kasa ya bayyana, ya samu gagarumin goyon baya

A gefe guda, mun kawo cewa kungiyar Arewa Solidarity Organisation (ASO) ta yi hasashen Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin wanda ya fi dacewa da takarar shugaban jam’iyyar All progressives Congress (APC)na kasa.

Mai magana da yawun ASO, Abdullahi Risky, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, ya lura cewa tsohon gwamnan na Borno shine wanda jam’iyya mai mulki ke bukata don samun babban matsayi, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Risky ya kara da cewa dan majalisan na tarayya yana da wayewa da gogewa a siyasar jam’iyya don inganta ka’idojin dimokuradiyya na APC.

Kara karanta wannan

Cikin hotuna: Matashi mai shekaru 25 da ya lashe kujerar shugaban matasan PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel