Goje ya yi kokarin tayar da tarzoma ne sai mutane suka bijire masa – Gwamna Inuwa Yahaya

Goje ya yi kokarin tayar da tarzoma ne sai mutane suka bijire masa – Gwamna Inuwa Yahaya

  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya yi zargin cewa Sanata Danjuma Goje ya yi kokarin tayar da tarzoma ne a jihar lokacin da mutane suka far masa
  • Goje dai ya zargi Inuwa Yahaya da aika masa yan baranda domin su halaka shi a lokacin da yake a hanyarsa ta shiga Gombe
  • Sai dai gwamnan ya bayyana cewa gaskiya za ta yi halinta bayan hukumomin da abun ya shafa sun kammala bincike kamar yadda sanatan ya bukata

Jihar Gombe - Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya zargi Sanata Danjuma Goje mai wakiltan Gombe ta tsakiya da kokarin haddasa tarzoma a jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

A makon da ya gabata ne wasu yan daba suka far ma Goje lokacin da yake a kan hanyarsa ta shiga garin Gombe.

Read also

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

Goje ya yi kokarin tayar da tarzoma ne sai mutane suka bijire masa – Gwamna Inuwa Yahaya
Goje ya yi kokarin tayar da tarzoma ne sai mutane suka bijire masa – Gwamna Inuwa Yahaya Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Sanatan ya zargi gwamnan da tura masa yan baranda a lokacin da ya ziyarci Gombe domin halartan wani taro nasa na kansa.

Da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati a ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba, Yahaya ya ce mutane sun nuna turjiya ne a kan kokarin Goje na haddasa rigima da karya doka da oda a jihar.

Ya ce:

"Hukumomin da abun ya shafa za su gano gaskiyar lamari tunda ya kai kara domin a binciki lamarin.
"Mu jira mu ga sakamakon binciken, amma duk wanda ya san tarihin Gombe, ya san wanene Goje sannan sun san wanene Inuwa. mutane sun san banbancin da ke tsakaninmu.
"Yanayin tsaro a jihata ya dawo yanzu kuma mutane na gudanar da harkokin gabansu. Tsohon gwamnan jihar, kuma sanata mai ci a yanzu da kuka sani, Danjuma Goje, shine ya haddasa halin da aka shiga kafin yanzu.

Read also

Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi a Gombe

"Ya yi kokarin tayar da tarzoma ne sai kuma mutane suka bijire ma hakan, amma sakamakon arangamar da aka yi, an rasa rayuka sannan an lalata kayayyakin wasu mutane. Wannan shine abun da bama so a matsayinmu na gwamnati."

Yahaya ya ce yana kokarin cika alkawarin da ya daukar ma mutanen Gombe na tabbatar da ci gaba mai dorewa a jihar, ruwayar Leadership.

Ya ce:

"Babban burina shine tsayawa da kafufuna da kuma cika alkawaran da na daukar ma mutane da kawo ci gaba a jiharmu, tare da zaman lafiya saboda idan babu zaman lafiya, toh ba za a samu ci gaba ba."

Kan ko za a bayar da damar yin sasanci, Yahaya ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci kowani yunkuri na kawo matsala a jihar ba.

Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi

Read also

Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi

A baya mun kawo cewa tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltan Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje ya nemi Sufeto Janar na 'yan sanda, Alkali Baba da babban Atoni Janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami da su binciki harin da aka kai masa.

Goje ya yi zargin cewa harin da aka kai masa a Gombe yunkuri ne na hallaka shi da hadiminsa, Adamu Manga.

Ya yi zargin cewa dogarin gwamna Inuwa Yahaya, Zulaidaini Abba da shugaban tsaron gwamnan, Sani Bajoga sune manyan wadanda ake zargi, rahoton Punch.

Source: Legit.ng

Online view pixel