Zaben Anambra 2021: Jam'iyyar APC ta maida martani kan zargin da ake mata game da zaben gwamna

Zaben Anambra 2021: Jam'iyyar APC ta maida martani kan zargin da ake mata game da zaben gwamna

  • Jam'iyyar APC ta musanta jita-jitar da ake jingina mata cewa ta bukaci hukumar INEC ta soke zaɓen Anambra
  • Shugaban APC reshen Anambra, Chief Basil Ejidike, yace ba dalilin da zai sa APC ta faɗi haka yayin da ake cigaba da zaɓe
  • Ya kuma shawarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ɗauki matakin gyara matsalolin da aka samu a wasu wurare

Anambra - Jam'iyyar APC a jihar Anambra ta yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa cewa ta bukaci a soke zaɓen gwamnan Anambra da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban APC reshen Anambra, Chief Basil Ejidike, shine ya bayyana haka a sakateriyar APC dake Awka, ranar Litinin, kamar yadda Vanguard ra rahoto.

Zaben Anambra 2021
Zaben Anambra 2021: Jam'iyyar APC ta maida martani kan zargin da ake mata game da zaben gwamna Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yace:

"Na yi mamakin jita-jitar dake yawo a kafafen sada zumunta cewa APC ta yi kira a soke zaɓen da aka gudanar, shugaban APC ya faɗi, kuma ya sha ƙasa a runfar zaɓen sa."

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2021: Akwai sauran rina a kaba, inji dan takarar PDP, Valentine

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Baki ɗaya jitar-jitar babu na gaskiya ko ɗaya, kuma ban yi wata magana makamanciyar wannan ba a kafafen watsa labari."

Akwai sauran zaɓe ba'a kammala ba

Shugaban APC ya kara da cewa ba yadda za'ai jam'iyya ta yi irin wannan kiran yayin da ake tsaka da zaɓe ba'a kammala ba.

Tribune Online ta rahoto yace:

"Babu dalilin da zai sa mu nemi a soke sakamakon zabe, wanda ake cigaba da gudanar wa ba'a kammala ba."
"Amma shawaran mu ga masu shirya zaɓen shine su gyara kuskuren da aka yi, saboda an samu matsaloli da dama a zaɓen ranar Asabar."

Wane wurare ne aka samu matsala?

Ejidike ya lissafa wuraren da yake zargin akwai matsala kamar Idemili ta arewa, baki ɗaya Orumba ta arewa, Anambra ta gabas, Ayamelum, Anambra ta yamma, Awka ta arewa da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Shugaban jam'iyyar APGA da ta lallasa APC, PDP a zaben Gwamnan Anambra ya magantu

A cewarsa abin takaicin shine duk da APC ta bada ƙorafin matsaloli, amma baturen zaɓe ya yi kunnen uwar shegu ya sanar da sakamakon zaɓen karamar hukumar Orumba ta arewa.

A wani labarin kuma kun ji Yadda fusatattun masu kada kuri'a suka garƙame ma'aikatan INEC a Anambra

Wasu mutane sun nuna fushinsu kan ma'aikatan INEC bayan kammala zaɓe ana tattara sakamako a karamar hukumar Orumba ta Arewa.

Rahoto ya bayyana cewa ma'aikatan ne suka nemi barin cibiyar tattara sakamakon gundumar Oko II domin su koma ofishin INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel