Dan takarar da ka iya zama shugaban APC na kasa ya bayyana, ya samu gagarumin goyon baya

Dan takarar da ka iya zama shugaban APC na kasa ya bayyana, ya samu gagarumin goyon baya

  • Kungiyar Arewa Solidarity Organisation (ASO) ta nuna cikakken goyon bayanta ga Ali Modu Sheriff gabanin babban taron APC na kasa
  • ASO ta riki ra’ayin cewa tsohon gwamnan na Borno shine mutumin da ya fi dacewa ya jagoranci jam’iyya mai mulki zuwa ga nasara a babban zaben 2023
  • Haka kuma, kungiyar ta arewa ta yi imanin cewa Sheriff zai iya ja da PDP, babbar jam’iyyar adawar APC

Kungiyar Arewa Solidarity Organisation (ASO) ta yi hasashen Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin wanda ya fi dacewa da takarar shugaban jam’iyyar All progressives Congress (APC)na kasa.

Mai magana da yawun ASO, Abdullahi Risky, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, ya lura cewa tsohon gwamnan na Borno shine wanda jam’iyya mai mulki ke bukata don samun babban matsayi, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Dan takarar da ka iya zama shugaban APC na kasa ya bayyana, ya samu gagarumin goyon baya
Dan takarar da ka iya zama shugaban APC na kasa ya bayyana, ya samu gagarumin goyon baya Hoto: Senator Ali Modu Sheriff
Asali: Facebook

Risky ya kara da cewa dan majalisan na tarayya yana da wayewa da gogewa a siyasar jam’iyya don inganta ka’idojin dimokuradiyya na APC.

Sanarwar ta kara da cewa Sanatan shine mutumin da ya dace ya tsaya a matsayin dakaru akan Peoples Democratic Party (PDP).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Risky ya ce:

"ASO ta kuma yi na’am da mara wa takararsa baya saboda kalaman da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kwanan nan cewa bai kamata a bar APC ta mutu bayan mulkinsa ba.
"A saboda haka, ASO ta yanke shawarar tallafawa Sheriff don ganin ya zama Shugaban Jam'iyyar na kasa saboda shi kadai ne wanda ke da abin da ya kamata don fuskantar PDP, wanda ke matukar son kawar da APC daga mulki a 2023.
Babban alherinsa a cikin PDP da sauran jam’iyyun adawa zai kara rage girma da arzikin sauran jam’iyyun siyasa zuwa ga APC.”

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya bayyana wani sirri mai ban dariya game da matarsa da diyarsa

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

A gefe guda, wani jigo a jam'iyyar APC na jihar Borno, Mustapha Gambo, ya ce tsohon gwamnan jihar, Sanata Ali Modu-Sheriff yana da abin da ake bukata domin sabonta APC idan ya zama shugaban jam'iyyar na kasa.

Gambo, wanda ya kasance mataimaki ga tsohon gwamnan jihar Borno, Ibrahim Shettima, ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da jaridar The Punch a Abuja, a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba.

Ya ce takardun shaidar zama dan kasuwa da dan siyasa mai zurfin tunani ya sa ya cancanci hawa matsayin babban mukami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng