Bayan ganawa da Buhari, Tinubu ya bayyana abinda suka tattauna a kai

Bayan ganawa da Buhari, Tinubu ya bayyana abinda suka tattauna a kai

  • Bola Tinubu, jigon jam'iyyar APC, ya ce ba batun siyasa suka tattauna da Buhari ba a ziyarar da ya kai masa
  • Tinubu ya ce ya ziyarci Buhari ne domin yi masa sannu da dawowa daga kasa mai tsarki kuma ya mika godiyarsa
  • Tsohon gwamnan jihar Legas din ya yi jinya a London kuma shugaba Buhari ya kai masa ziyara, ya ce ya matukar jin dadin haka

FCT, Abuja - Bola Tinubu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce babu batun siyasa da suka tattauna a ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kasan ya karba bakuncin tsohon gwamnan jihar Legas a fadarsa da ke Aso Villa a ranar Lahadi.

TheCable ta ruwaito cewa, su biyun sun hadu a gidan shugaban kasan kafin su garzaya tare da shiga ganawar sirri.

Kara karanta wannan

Ka hanzarta ceto nagartar ka, wadanda ka yarda da su ke batar da kai, Dalung ga Buhari

Tinubu ya ce dalilin zuwansa shi ne zuwa sannu da zuwa ga shugaban kasan kan tafiyar da yayi zuwa Saudi Arabia inda yayi Umrah.

Bayan ganawa da Buhari, Tinubu ya bayyana abinda suka tattauna a kai
Bayan ganawa da Buhari, Tinubu ya bayyana abinda suka tattauna a kai. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya ce, ya yi godiya ga shugaban kasan kan ziyarar da ya kai masa a London yayin da ya ke jinya.

"Kawai na mika godiya ta ga shugaban kasa, na farko kan ziyarar da ya kai min gidana da ke London bayan aikin da aka yi min da kuma karfafa min guiwa da yayi. Babu shakka shugaba ne na daban.
"Don haka ne na zo kuma in yi masa barka da dawowa daga kasa mai tsarki," Tinubu yace bayan ganawarsu.
"Ba siyasa ba ce, ziyara ce kawai domin in gode masa, shikenan," Tinubu yace kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso

Jigon jam'iyyar APC ya dawo kasar Najeriya a ranar 9 ga watan Oktoba bayan kwashe watanni da yayi a London ya na jinyar kafa da aka yi masa aiki.

A yayin da ya ke Ingila, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai wa Tinubu ziyara.

Duk da har a halin yanzu Tinubu bai fito fili ya bayyana bukatarsa ta fitowa takarar shugabancin kasa a shekarar 2023 ba, ana ta kaddamar da kungiyoyin gangamin neman zabe da sunansa.

Bola Tinubu ya dira Aso Villa, Yace shugaba Buhari na musamman ne

A wani labari na daban, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, a fadarsa dake Abuja, ranar Lahadi da safe.

Mai taimakawa shugaban ƙasa Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, shine ya sanar da haka a shafinsa na dandalin Facebook.

Bashir Ahmad ya rubuta kamar haka:

"Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin jagoran babbar jam'iyyar mu APC, Asiwaju Bola Tinubu, a gidan gwamnati dake Abuja, da safiyar yau."

Kara karanta wannan

Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel