Ka hanzarta ceto nagartar ka, wadanda ka yarda da su ke batar da kai, Dalung ga Buhari

Ka hanzarta ceto nagartar ka, wadanda ka yarda da su ke batar da kai, Dalung ga Buhari

  • Tsohon ministan Buhari ya yi kira gare shi da ya hanzarta ceto nagartarsa saboda wadanda ke zagaye da shi ne ke batar da shi
  • Solomon Dalung, tsohon ministan matasa da wasanni, ya ce Buhari ya na fama da matsalar bacin suna saboda wakilansa ba su yin abinda ya dace
  • Dan asalin jihar Filaton ya ce, kalubalen shugabanci sun mamaye shugaba Buhari kuma makusantansa ba su da manufa irin ta shi

Jos, Filato - Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya ce tsohon ubangidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na fama da matsalar bacin suna saboda wadanda ya yarda da su ba su yin abinda ya dace.

Dalung, wanda ya yi aiki karkashin Buhari a matsayin minista daga 2015 zuwa 2019, ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya yi kira ga shugaban kasar da ya gaggauta kai wa nagartarsa dauki.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso

Ka hanzarta ceto nagartar ka, wadanda ka yarda da su ke batar da kai, Dalung ga Buhari
Ka hanzarta ceto nagartar ka, wadanda ka yarda da su ke batar da kai, Dalung ga Buhari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya kara da shawartar shugaban kasan kan ya sani cewa nagartarsa kadai ba za ta iya ceto kasar nan ba matukar wadanda ya bai wa mukamai suna yin abinda bai dace ba.

Wani sashi na wallafar ta ce, "Idan kowa na sauke nauyin da ke kansa cike da gaskiya, tabbas gaskiyar halinka da dabi'un ba za su bayyana ba ma tun farko. Tunda ya dogara da su wurin mulki, labaransu gaskiya ne a wurin ka wanda kuma akasin hakan ne a bayyane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kalubalen shugabanci sun ci galaba a kan ka da kuma tsananin bukatar taimako, amma abun takaicin shi ne yadda ka ke zagaye da mutanen da manufar ku ba daya bace ba."

Dalung ya ce shugaban kasa ya dace ya sani cewa, ba zai iya sauke nauyin da ke kansa na shugabancin kasa shi kadai ba saboda yawan abinda ke gabansa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi

Na kusa da Buhari suna kangeshi da masu fada masa gaskiya, Dalung

A wani labari na daban, tsohon ministan wasanni da harkokin matasa, barista Solomon Dalung, ya koka kan yadda wasu makusanta shugaban kasa Muhammadu Buhari a mulki suke kange shi da masu kokarin ganin sun daura shi a turba ta gari da yi wa 'yan kasa hidima.

Dalung ya kuma bayyana cewa, na kusa da shugaban sukan ba da uzurin bogi na cewa, akwai annobar Korona don haka ba za a iya gana wa da shugaban ba.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da wakilinmu a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel