Zargin komawa APC: Jonathan bai halarci taron gangamin PDP ba, ya cilla kasar waje

Zargin komawa APC: Jonathan bai halarci taron gangamin PDP ba, ya cilla kasar waje

  • Yayin da ake ci gaba da taron gangamin PDP a Abuja, tsohon shugaban kasa Jonathan bai halarci taron ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa, Jonathan zai tafi kasar waje domin halartar wani taron zaman lafiya a kasar Kenya
  • Ana ta rade-radin tsohon shugaban kasar zai koma APC, tare da yiyuwar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023

Ana ta cece-kuce a ranar Asabar, 30 ga watan Oktoba a wurin taron gangamin jam'iyyar PDP na kasa, Abuja, inda tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan bai halarta ba.

Rahotanni sun ce akwa rade-radin cewa Goodluck na shirin shiga jam’iyyar APC mai mulki da kuma zama dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023.

Da dumi-dumi: Jonathan bai halarci taron gangamin PDP ba, ya cilla kasar waje
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan | Hoto: bbc.com

Jonathan dai ya sha musanta irin wannan batu sau da dama inda ya ce ya mayar da hankali ne wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da ci gaban kasar.

Read also

Da duminsa: Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli a Abuja

Sai dai kuma an tattaro cewa a halin yanzu Jonathan na kan hanyarsa ta zuwa birnin Nairobi na kasar Kenya domin halartar wani babban taron kungiyar Tarayyar Afirka na zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a Afirka.

Jonathan wanda shi ma jigo ne a kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS a kasar Mali kuma shugaban kungiyar masu hikimar ECOWAS zai kasance a kasar Kenya na tsawon kwanaki 3.

Taron da zai halarta an yi masa taken: "Ingantaccen Hadin kai da daidaituwa don Sasanci Mai Tasiri".

Mai ba Jonathan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ikechukwu Eze, ya bayyana tafiyar mai gidan nasa ne a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar, ya ce taron zai hada da shugaban hukumar, manyan jami’an gwamnatin Kenya, haka nam da kuma wakilan kasashe mambobin kungiyar AU, da kungiyoyin shiyya-shiyya, hukumomin kasa da kasa da sassan AU.

Read also

Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu

Legit.ng ta ruwaito sanarwar na cewa:

"Hakanan za ta ba wa mahalarta damar yin tunani, yin nazari da kuma duba kokarin shiga tsakani da ke gudana a cikin yanayin rikice-rikice a nahiyar, domin samun ingantaccen daidaituwa da samun tasiri mai dorewa."

Ya yi nuni da cewa, bayanan baya-bayan nan da kungiyar ta AU ta fitar, ta bayyana babban taron na shekara-shekara a matsayin daya daga cikin muhimman tsare-tsare na nahiyar don inganta tasiri wajen magance matsalolin rikice-rikice a Afirka.

Taron Gangamin PDP: Fastoci sun bayyana, Bala da takarar shugaban kasa, Shehu Sani kuma gwamna

A bangare guda, Dandalin Eagle Square, wurin da ake gudanar da taron gangamin jam’iyyar adawa ta PDP, a halin yanzu yana cike da tutoci da fastocin talla daban-daban na ‘yan takarar siyasa.

Wasu daga cikin fastocin sun hada da na gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar.

Read also

Allah Ya yiwa marubucin littafin 'Kulba na barna', Umaru Kasagi, rasuwa

Hakazalika da tsohon dan sanata, Shehu Sani; Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas; Doyin Okupe; Gwamna Aminu Tambuwal da sauran su.

Source: Legit.ng

Online view pixel