Gwamna Lalong ya yi martani, ya nuna kaduwa kan tsige kakakin Filato

Gwamna Lalong ya yi martani, ya nuna kaduwa kan tsige kakakin Filato

  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya nuna kaduwa matuka kan tsige Abok Ayuba a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar
  • Lalong ya ce sauyin da aka samu ya zo masu a bazata amma kuma cewa za su mutunta hukuncin majalisar kasancewarta mai iko da harkokinta
  • Ya fadi hakan ne a lokacin da sabon kakakin majalisar jihar, Rt. Hon. Yakubu Sanda ya kai masa ziyarar bangirma a gidan gwamnati

Jihar Filato - Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya yi martani kan tsige Abok Ayuba a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar. Ya bayyana cewa ya yi mamaki matuka a kan al’amarin.

A ranar Alhamis, 28 ga watan Oktoba ne takwas daga cikin yan majalisar 24 suka tsige Abok, wanda ke wakiltan mazabar Jos ta gabas.

Gwamna Lalong ya yi martani, ya nuna kaduwa kan tsige kakakin Filato
Gwamna Lalong ya yi martani, ya nuna kaduwa kan tsige kakakin Filato Hoto: The Plateau State Governor’s Directorate Of Press
Source: Facebook

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Rukuba/Irigwe, Musa Agah ne ya tabbatar da hakan.

Read also

Yadda yan majalisun PDP da APC suka fafata wajen tsige shugaban majalisar dokokin Filato

Agah ya ce yana a harabar majalisar lokacin yan majalisar suka aiwatar da tsigewar yayin da Jami’an tsaro suka hana masu adawa da tsige shi shiga harabar majalisar.

Amma da yake magana a lokacin da sabon kakakin majalisar, Yakubu Sanda ya ziyarce shi a gidan gwamnati, gwamnan ya dage cewa yan majalisa 16 ne suka sanya hannu don tsige taohon kakakin, rahoton Punch.

Wata sanarwa daga daraktan harkokin labarai na gwamnan, Macham Makut, ya ce:

“Sabon kakakin majalisar dokokin jihar Filato Rt. Hon. Yakubu Sanda ya jagoranci jami’ansa da sauran mambobin majalisar zuwa gidan gwamnati domin ba bangaren zartarwa tabbacin samun hadin kansu wajen gudanar da harkokin jihar.
“Sabon kakakin ya samu tarba daga sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Danladi Abok Atu a madadin gwamnan.

Read also

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

“Da yake magana a yayin ziyarar, Shugaban masu rinjaye a majalisar Hon. Naanlong Daniel ya ce sun zo gidan gwamnati ne daidai da al’adar majalisar don gabatar da sabon shugaban majalisar a duk lokacin da aka samu canji."

Jawabin ya kara da cewa sabon kakakin majalisar ya bayyana bayan 16 daga cikin mambobin majalisar 23 sun sanya hannu a korafi don tsige tsohon kakakin majalisar.

Da yake martani a madadin gwamnan, sakataren gwamnatin jihar Filato, Farfesa Danladi Abok Atu ya ce Gwamna Lalong da gaba daya yan majalisarsa sun yi mamakin ci gaban .

Sai dai ya ce duk da hakan sun mutunta hukuncin majalisar wacce ta kasance da ikon kula da harkokinta na cikin gida, Leadership ta rahoto.

Ya ba majalisar tabbacin cewa kofofi a bude suke a koda yaushe domin hada gwiwa tsakaninsu wajen isar da shugabanci nagari da tabbatar da ajandar ceto.

Kakakin ya samu rakiyar mataimakin kakakin majalisar Shehu Sale Yipmong, shugaban masu rinjaye da sauransu.

Read also

Rikicin majalisar malaman Kano: Daga karshe Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu

Yadda yan majalisun PDP da APC suka fafata wajen tsige shugaban majalisar dokokin Filato

Da farko mun kawo cewa majalisar dokokin jihar Filao ta tsige kakakinta, Honorabul Abok Ayuba Nuhu.

Rahoto ya bayyana cewa an maye tsohon kakakin da Honorabul Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana, karamar hukumar Bassa, jihar Filato.

Source: Legit.ng

Online view pixel