Da Duminsa: Wani tsohon gwamna zai shigo jam'iyyar PDP nan kusa, inji Fintiri

Da Duminsa: Wani tsohon gwamna zai shigo jam'iyyar PDP nan kusa, inji Fintiri

  • Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya ce tsohon gwamna Mimiko na shirin shigowa jam'iyyar adawa ta PDP
  • Kalaman gwamnan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ce nan ba da jimawa ba wani tsohon gwamna zai shigo jam’iyyar PDP
  • Mimiko wanda tsohon gwamnan jihar Ondo ne a halin yanzu fitaccen dan jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ne

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ce nan ba da dadewa ba, Olusegun Mimiko tsohon gwamnan jihar Ondo zai sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a lokacin da ya bayyana a matsayin a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.

Read also

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

Da Duminsa: Wani tsohon gwamna zai shigo jam'iyyar PDP nan kusa, inji Fintiri
Gwamnan jihar Adamawa, Fintiri | Hoto: thenationonlineng.net
Source: Facebook

Da yake mayar da martani kan furucin cewa PDP ta rasa wasu daga cikin gwamnoninta zuwa jam’iyyar APC mai mulki, Fintiri ya ce ba a cin zabe bisa yawan gwamnonin da jam’iyya ke da su.

Sai dai ya yi takama da cewa wasu fitattun ‘ya’yan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP gabanin zabe mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalaman na gwamna Fintiri na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ce nan ba da dadewa ba wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da wani tsohon gwamna za su sauya sheka zuwa PDP.

Tsohon gwamnan na Kwara ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Arise News TV inda yake cewa:

"Muna da wasu manya da za su shigo jam'iyyar. A wannan makon, akwai wani tsohon gwamna da zai koma jam’iyyar. Muna da da yawa da suka shigo."

Read also

Wani dan majalisa ya koma jam'iyyar PDP ana saura kwana 11 zabe a Anambra

Legit.ng ba ta iya tantance ko tsohon gwamna Mimiko da Fintiri ya ambata shi ne wanda Saraki ke magana akai ba.

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Adamawa, ya ce zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar baya idan ya sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa, Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.

Gwamnan na jihar Adamawa ya ce Atiku na da dukkan abubuwan da ya kamata na mulkin Najeriya, yana mai jaddada cewa zai yi kokarin ganin ya zama shugaban Najeriya idan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Read also

Saraki: Kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa PDP

Source: Legit

Online view pixel