Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya fice daga cikin jam'iyyar, ya bayyana dalilai

Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya fice daga cikin jam'iyyar, ya bayyana dalilai

  • Wani babban jigon jam'iyyar APC a jihar Yobe, ya miƙa takardar ficewarsa daga cikin jam'iyyar kan wasu dalilii
  • Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin APC a 2023, Alhaji Aji Kolomi, yace ya ɗauki wannan matakin ne a karan kansa
  • A cewarsa duba da yanayin da jam'iyya ke ciki a yanzu, ya ga ya dace ya fice daga cikinta

Yobe - Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Yobe ƙarƙashin APC, Alhaji Aji Kolomi, ya yi murabus daga jam'iyyar APC a hukumance, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A wata wasiƙa da ya aike wa shugaban APC na gundumar Ngurbuwa, ƙaramar hukumar Gubja, jihar Yobe, Aji yace:

"Bayan girmama wa gareka, ina mai sanar da kai cewa na ɗauki matakin yin murabus daga jam'iyyar AOC bisa ratsin kaina."

Read also

Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

"Ina miƙa godiya ta gare ka da sauran yan majalisar zartarwa bisa goyon bayan da kuka nuna mun lokacin neman takara ta a 2019, Nagode sosai."
Jihar Yobe
Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya fice daga cikin jam'iyyar, ya bayyana dalilai Hoto: punchng.com
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa ya fita daga APC?

Mista Aji ya ƙara da cewa ya yanke wannan hukuncin ne a karan kansa da kuma yanayin tafiyar gwamnatin APC.

"Duba da yanayin siyasar dake faruwa a cikin jam'iyyar APC, daga yau Litinin 18 ga watan Oktoba na yi murabus daga APC, ga katin zama ɗan jam'iyya nan na haɗo da shi."

Shugabanni ku ji tsoron Allah - Aji

Tsohon jigon APC ya kuma roki shugabannin da aka zaɓa su saka Allah a ransu wajen sauke nauyin da al'umma ta ɗora musu.

A cewarsa za'a samu cigaba ne a mulkin demokaraɗiyya idan masu rike da madafun iko sun tabbatar da sauke nauyin dake kansu ba tare da nuna ban-banci ba.

Read also

Siyasar Kano: Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje

A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Vandeikya, jihar Benuwai.

Dailytrust ta rahoto sanata mai wakiltar Benuwai ta kudu, Abba Moro, na cewa jam'iyyarsa ta PDP ce kaɗai zata iya magance matsalolin Najeriya.

Source: Legit

Online view pixel