Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
- Wasu manyan jiga-jigan APC tare da dubbannin magoya bayansu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Benuwai
- Sanata Abba Moro, yace jam'iyyar PDP ce kaɗai zata iya ceto Najeriya daga halin da APC ta jefa ta idan ta samu dama a 2023
- Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya yabawa masu sauya shekan, yace ba za'a nuna musu banbanci ba
Benue - Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Vandeikya, jihar Benuwai.
Dailytrust ta rahoto sanata mai wakiltar Benuwai ta kudu, Abba Moro, na cewa jam'iyyarsa ta PDP ce kaɗai zata iya magance matsalolin Najeriya.
Sanatan, wanda ya yi jawabi wajen bikin tarbar masu sauya sheƙan, yace Najeriya ta rasa komai ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Sanata Moro yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Jam'iyyar PDP ce kaɗai zata iya ceto Najeriya daga halin da take ciki idan ta sake samun dama a 2023."
Ba zamu nuna muku banbanci ba, Ortom
Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yin karbar sabbin yan PDP, ya tabbatar musu cewa ba za'a nuna musu banbanci ba.
Ya kara jaddada yaƙininsa cewa jami'iyyar PDP zata sake kwace mulki a babban zaɓen 2023 dake tafe domin ceto Najeriya.
Suwaye jiga-jigan APC da suka koma PDP?
Gwamnan ya kuma bayyana sunayen waɗanda suka sauya sheƙan da suka haɗa da, Joseph Kyaagba, Chief Joe Akaakar, John Actsu; da Barista Michael Gwaza.
Manyan jiga-jigan sun jagoranci dubbannin magoya bayansu wajen ficewa daga APC da komawa PDP.
Wani irin hali APC ta jefa Najeriya?
Gwamna Ortom ya koka kan yadda yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa wanda mulkin APC ya jawo musu.
Ya kuma ƙara da cewa jam'iyyar APC ta jefa yan ƙasa cikin wani hali da basu taba gani ba tun bayan dawowar mulkin demokaradiyya.
A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shine abin damuwa ba.
Atiku yace babu wani abu shugaban ƙasa daga kudu ko daga arewa, abinda duniya ta sani shine shugaban Najeriya.
Asali: Legit.ng