Rarara ya bada shawarar a kyale Buhari ya cigaba da mulki har zuwa shekarar 2027 ko 2028

Rarara ya bada shawarar a kyale Buhari ya cigaba da mulki har zuwa shekarar 2027 ko 2028

  • Dauda Adamu Kahutu zai so Muhammadu Buhari ya yi ta mulki har zuwa 2027
  • Babban mawakin yana ganin zai yi kyau a karawa Buhari shekaru hudu ko biyar
  • A wata hira da aka yi da shi, Rarara ya fadi sirrin kaunar da yake yi wa Buhari

Katsina - Dauda Adamu wanda aka fi sani da Rarara, ya yi hira ta musamman da BBC Hausa, inda ya tabo batutuwan siyasa da yadda yake shirya wakoki.

Shahararren mawakin ya bayyana cewa akwai bukatar a bar Muhammadu Buhari ya cigaba da mulki.

Da yake bayanin rayuwarsa, an ji cewa an haifi fitaccen mawakin ne a garin Kahutu, karamar hukumar Danja, a jihar Katsina, ya kuma dade a waka.

A wannan hira da aka yi da mawakin, aka kuma wallafa a ranar 24 ga watan Oktoba, 2021, yace zai yi kyau a kyale Buhari ya karasa ayyukan da ya fara.

Read also

Siyasar Kano: Kwankwaso ya bayyana ra'ayinsa kan tafiya da Shekaru a siyasa

A bar Gwamnatin Buhari ta cigaba da ci

“Idan Buhari ya gama ka’idojin mulkinsa, idan ta ni za a bi, da za ayi shawara da ni, akwai bukatar a kara masa shekaru hudu ko biyar.” – Dauda Rarara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Saboda abubuwan da ya turo su gama, ya kammala su. Amma wannan nawa ra’ayin kenan.”
“Amma na san idan na fito da abin da na gani, su ma za su hau kan wannan layin."
Dauda Rarara
Rarara, Buhari da wasu Mawaka Hoto: thenewsnigeria.com.ng
Source: UGC

Meyasa Rarara yake yi wa Buhari waka?

Har ila yau, da aka tambayi Dauda Adamu Kahutu Rarara dalilin da ya sa yake yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari waka, sai yace gaskiyarsa.

“Tun da nake karami sosai ake ce mani Buhari ne mai gaskiya, har yau ban ji kishiyar haka ba.” - Rarara
"Ba nayi Buhari don ya bani wani abu ba, ba na yi shi domin in samu kudi ba. Ba na yi shi domin in samu mukami ba. Na yi domin yana kishin kasa ta” – Rarara.

Read also

Gwamnatin Buhari na tunanin yin afuwa ga mutanen da Janar Abacha ya bindige a 1995

Mawakin ya bayyana cewa ya yi wa Buhari wakoki har 66, amma a ciki yace ‘Sai Baba Buhari’ ce bakandamiyarsa, duk da an fi sanin shi da ‘Masu gudu, su gudu.'

Rarara ya shaidawa BBC Hausa cewa akwai wanda ya taba yi masa tayin Naira miliyan 500 domin ya daina yi wa Buhari waka, amma ya ki karbar wannan tayi.

Muslim Rights Concern ta na so Musulmin Bayarabe ya karbi mulki

Dazu kun ji cewa Kungiyar addinin muslunci ta Muslim Rights Concern wanda aka fi sani da MURIC, ta tsoma baki game da siyasa da wanda za a ba mulki a 2023.

MURIC ta fitar da jawabi a ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, 2021, tana bayyana sha’awarta na ganin an samu Bayarabe kuma musulmi a kan mulki bayan Buhari.

Source: Legit.ng News

Online view pixel