Atiku Abubakar: An tura mahaifi na gidan yari don ya ƙi yarda in yi makarantar boko

Atiku Abubakar: An tura mahaifi na gidan yari don ya ƙi yarda in yi makarantar boko

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce mahaifinsa ya tafi gidan yari saboda hana shi zuwa makaranta
  • Turakin Adamawa ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa wurin taron yaye daliban jami'ar Baze a ranar Juma'a a Abuja
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya shawarci daliban da aka yaye su yi amfani da ilimin su wurin taimakawa sauran mutane

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya magantu kan yadda aka tura mahaifinsa gidan yari saboda ya ki saka shi a makarantar boko, rahoton The Punch.

Amma, Atikun ya ce daga bisani mahaifinsa ya kyalle shi ya tafi makarantar, ya kara da cewa kyauta ya yi karatu duk da cewa iyayensa ba masu hannu da shuni bane.

Atiku Abubakar: An tura mahaifi na gidan yari don ya ƙi yarda in yi makarantar boko
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi wurin bikin yaye dalibai a Jami'ar Baze da ke Abuja a ranar Juma'a.

A makallarsa mai taken 'warware kallubalen ilimi a Nigeria', Atiku ya ce lokacin yana yaro ya kan kwashi dabobin makwabtansa ya tafi daji kiwo don a bashi hatsi ya bawa kakakinsa a ciyar da gida.

An tura mahaifi na gidan yari don ya hana ni zuwa makarantar boko

A cewarsa:

"Ni dan makaranta ne kuma makiyayi, ni na ke ciyar da gidan mu.
"Duk da cewa iyaye ba masu kudi bane, na yi karatu a kyauta, biya na ma ake yi in tafi makaranta. Da farko, mahaifi na baya son in tafi makaranta, hakan yasa aka tura shi gidan yari. Na cigaba da karatu a wasu manyan makarantu. Ni ne shugaban kungiyar dalibai a makarantar koyon tsafa, Kano."

Atiku ya cigaba da cewa a lokacin yana da shekaru 11, mahaifinsa ya rasu yayin kokarin tsallaka rafi. Bai kai shekaru 40 ba kuma shi kadai ne iyayensa suka haifa. Don haka wurin kakakinsa ya girma wasu lokutan da kyar suke iya cin abinci sau daya a rana.

Kara karanta wannan

Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat

Ku yi amfani da iliminku wurin tallafawa al'umma

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa kowa abin da Allah ya kadara masa a rayuwa daban ne, wasu iyayensu na da kudin biya musu kudin makaranta amma muhimmin abu shine a samu ilimin a kuma tallafawa wasu suma su samu.

Atiku, wanda shine dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2019, ya ce ba domin karatun da ya yi ba, akwai yiwuwar ba zai kai matsayin da ya kai a yanzu ba a rayuwa.

Turakin Adamawan ya shawarci daliban da aka yaye su yi amfani da ilimin da suka samu wurin tallafawa sauran mutane, kuma maza da mata dukkansu suna bukatar ilimi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel