Taron gangami na ƙasa: PDP ta dakatar da mutane 3 daga yin takara

Taron gangami na ƙasa: PDP ta dakatar da mutane 3 daga yin takara

  • Kwamitin tantancewa ta dakatar da mutane 3 takara bisa rashin cancanta
  • An samu rahoto akan yadda ‘yan takarar har kotu su ka maka jam’iyyar
  • Shugaban kwamitin rikon kwarya, Ahmadu Fintiri ne ya bayyana hakan ranar Alhamis

Abuja - Kwamitin tantancewar jam’iyya PDP ta tarayya ta bayyana yadda ta hana mutane 3 takarar zaben ranar 30 da 31 ga watan Oktoba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Shugaban kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da tambarin jam’iyyar da ababen cigaban ta a ranar Alhamis a Abuja.

Taron gangami na ƙasa: PDP ta dakatar da mutane 3 daga yin takara
Magoya bayan jam'iyyar PDP: Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Read also

Rikicin PDP na kara kamari yayin da ta hana wasu fitattun mambobi 3 tsayawa takara

Antoni janar kuma ministan shari’a na kasa, Mohammed Adoke ne shugaban kwamitin.

Fintiri ya ce kwamitin ta kammala aikin ta na tantance ‘yan takara kuma ta mika rahoton ta ga kwamitin shiryawa a ranar Alhamis da rana.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, ya kula da yadda ‘yan takara 31 su ke neman makamai daban-daban a jam’iyyar, cikin su 27 ne su ka sha yayin da aka dakatar da mutane 3.

Ya bayyana yadda wadanda aka hana takarar akwai Wale Oladipo, Okey Muo-Aroh da Eddy Olafeso.

Oladipo ya na neman kujerar mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu, yayin da Messrs Muo-Aroh ya ke naman kujerar babban sakataren jam’iyyar na kasa sai Olafeso kuma sakataren watsa labarai na kasa.

Kamar yadda yace:

“An dakatar da duk wadannan ‘yan takarar ne saboda sun maka jam’iyya a kotu. Kuma sun so a hana gangamin jam’iyyar na kasa.
“Ka kai jam’iyya kotu ba tare da an gama magana tun a cikin gida ba, ka na so ne ka dakatar da gangamin jam’iyya gaba daya kenan.”

Read also

Hakimi a Yobe ya hadu da fushin gwamna bayan da ya narkawa gwamnan ashariya

Fintiri ya ce dole jam’iyyar PDP ta ladabtar

Ya bayyana yadda wajibi ne jam’iyya ta ladabtar da duk wanda ya yi abinda be dace ba. Kuma duk wanda be yarda da hukuncin ba zai iya daukaka kara kafin ranar Juma’a.

Fintiri ya kara da bayyana bukatar kamatar jam’iyyar ta zabo wadanda su ka dace don tafiyar da al’amuran ta cikin kwarewa da nagarta.

Ya bukaci ‘yan kwamitin su kasance ma su sadaukarwa wurin ganin an samu ci gaban gangamin.

Sakataren watsa labaran jam’iyyar PDP na tarayya, Kola Ologbondiyan, ya ce kwamtitin gangamin jam’iyyar wacce Fintiri ke shugabanta ta shirya yin gangamin da zai samar da tarin nasarori a zaben 2023.

Source: Legit.ng

Online view pixel