Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

  • Bayan gabatar da taron gangamin APC a jihohi, alamu sun nuna akwai matsaloli a jam'iyyar
  • An samu rarrabuwar kai, har aka samu wuraren taron biyu a wasu jihohi a fadin kasar
  • A jihar Adamawa, ana kyautata zaton 'yan tsagin Aisha Buhari ne za su lashe kujerun takarar

Adamawa - Jerin sunayen 'yan takarar hadin kai da ake zargin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta amince da su a matsayin 'yan takarar jam'iyyar APC na jihar Adamawa ne aka yanke hukuncin sun yi nasara a zaben shugabancin APC na jihar.

SaharaReporters ta rahoto cewa dukkan masu takarar da sunayensu ke cikin jerin hadin kai nan ba da jimawa ba za a bayyana su a matsayin wadanda suka yi nasara a taron gangamin jam'iyyar da aka yi a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

Da dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa
Jam'iyyar APC mai mulkin kasa | Hoto: officalAPC
Asali: UGC

Yayin da al'amura ke tafiya ta hanyar tsarin zabe, kuri'un da aka kada ya zuwa yanzu sun nuna cewa 'yan takarar da Uwargidan Shugaban kasa ke tallafawa sune wadanda aka zaba a taron gangamin.

Misali, Ibrahim Bilal, shugaban APC na jihar, wanda Aisha Buhari ke goyan baya, ya samu kuri'u 1,640 inda ya doke abokin karawarsa, Vrati Nzonzo, wanda ya samu kuri'u 224.

Gangamin taron APC na Jihohi: Gwamna Ganduje ya kafa sabon sharadi ga 'yan takara a jihar Kano

Tun kafin fara taron a Kano, gwamnatin Ganduje tace duk wani mamban jam'iyyar APC dake neman wani mukamin jam'iyya sai ya yi gwajin shan miyagun kwayoyi.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammad Garba, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Jam'iyyar APC ta ƙasa ta shirya gudanar da gangamin taronta na jihohi wanda za'a zaɓi shugabanni a matakin jiha ranar 16 ga watan Oktoba.

Kwamishinan ya shawarci dukkan yan takara da su je ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ranar Talata da misalin ƙarfe 7:00 na safe.

Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

A bangare guda, jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta gudanar da taron gangami na jihohi a ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba, inda aka yi zaben shuwagabannin jam'iyyu na jihohi a fadin Najeriya.

sai dai, jihohi da yawa sun ga sabon lamari tare da fitowar mambobi biyu na zartarwa yayin da jam’iyya mai mulki ke fafutukar ganin ta gyara gidanta kafin 2023.

A kasa mun kawi jerin jahohin da jam'iyyar APC mai mulki ta samar da wakilan zartarwa guda biyu sabanin daya da ya dace.

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel