Da dumi-dumi: Gwamna Buni ya yi sauye-sauye a majalisarsa, ya kafa sabuwar ma’aikata

Da dumi-dumi: Gwamna Buni ya yi sauye-sauye a majalisarsa, ya kafa sabuwar ma’aikata

  • Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya yi sabbin sauye-sauye a majalisarsa
  • Gwamnan ya sauya wa wasu kwamishinoninsa wuraren aiki sannan ya samar da sabuwar ma'aikata
  • Hkazalika an shafe ma'aikatar filaye da ma'adinai a jihar ta Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni yayi sauye-sauye a majalisarsa sannan ya kuma kafa sabuwar ma’aikata.

Buni ya sauya wa Abdullahi Bego wurin aiki daga ma’aikatar harkokin cikin gida, labarai da al’adu zuwa sabon kwamishinan ma’aikatar samar da dukiya, tallafi da aikin yi.

Da dumi-dumi: Gwamna Buni ya yi sauye-sauye a majalisarsa, ya kafa sabuwar ma’aikata
Da dumi-dumi: Gwamna Buni ya yi sauye-sauye a majalisarsa, ya kafa sabuwar ma’aikata Hotto: Daily Trus
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kuma mayar da Mohammed Lamin, kwamishinan ma’aikatar filaye da ma’adinai zuwa ma’aikatar harkokin cikin gida, labarai da al’adu.

Gwamnan a wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Baba Malam Wali, ya kuma soke ma’aikatar filaye da ma’adinai, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye da ma'aikatu: Matawalle ya ƙirƙiri sabbin ma'aikatu 4, ya sauya wa kwamishinoni wurin aiki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Haka nan, gwamnan ya kuma amince da cewa hakkin gudanar da lamuran filaye a cikin jihar ciki har da batutuwan da suka shafi rabon filaye, rajistan mallakar filaye, amfani, bincike, zane da tsare-tsare da sauran abubuwa da gwamnan zai yanke zuwa ga hukumar kula da tsarin bayanan kasa na Yobe (YOGIS).
“Saboda haka an shigar da aikin ma’aikatar filaye cikin hukumar YOGIS. Da wannan ci gaban, an shafe wanzuwar ma’aikatar filaye da ma’adinai a jihar Yobe."

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya yi garanbawul ga wasu mukaman jami'an gwamnatinsa ta jihar Kaduna.

Gwamnan ya bayyana sabbin sauye-sayuen ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, an yi sauye-sauyen don ciyar da bangarori daban-daban na gwamnatin gaba.

Kara karanta wannan

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

A cikin sanarwar da ta iso hannun Legit.ng Hausa, gwamnan ya ce, an yiwa kwamishinoni takwas daga cikin 14 sauyin ma'aikatu, inda wasu kuma sauyin bai shafi su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel