Jerin sunaye da ma'aikatu: Matawalle ya ƙirƙiri sabbin ma'aikatu 4, ya sauya wa kwamishinoni wurin aiki

Jerin sunaye da ma'aikatu: Matawalle ya ƙirƙiri sabbin ma'aikatu 4, ya sauya wa kwamishinoni wurin aiki

 • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya amince da kafa wasu ma’aikatu 4 na daban a jihar
 • Bayan kafa ma’aikatun ya kuma zabo sabon kwamishina ga ko wacce sabuwar ma’aikata
 • Ya kafa ma’aikatar kula da dajika da dabbobin kiwo, da ta samar da dukiya da ayyukan yi da sauran biyu

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya tabbatar da samar da ma’aikatu 4 sannan ya zabo sababbin kwamishinoni na ma’aikatun.

Ya bayyana hakan ne ta wata takarda wacce sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya bayyana a Gusau ranar Litinin bisa ruwayar The Punch.

Jerin sunaye da ma'aikatu: Matawalle ya ƙirƙiri sabbin ma'aikatu 4, ya sauya wa kwamishinoni wurin aiki
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara. Hoto: The Punch
Source: Facebook

A cewar Balarabe, ma’aikatun da ya kafa guda 4 su ne:

Read also

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

 • Ma’aikatar kula da dazuka da bunkasa kiwon dabobbi
 • Ma’aikatar samar da dukiya da kuma samar da ayyuka.
 • Ma’aikatar yawon bude ido da kula da otal da kuma
 • Ma’aikatar gina gidaje da bunkasa birane

Balarabe ya bayyana yadda gwamnatin ta nada sababbin kwamishinoni wadanda za su fara aiki daga nadin.

Ya lissafo ma’aikatun da kwamishinonin kamar haka;

 1. Ahmed Anka - Ma’aikatar ilimin kimiyya da fasaha
 2. Abubakar Dambo - Ma’aikatar harkokin kananun hukumomi
 3. Muh’d Magaji - Ma’aikatar al’adu
 4. Nasiru Masama - Ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni
 5. Abdulaziz Nahuce - Ma’aikatar ayyuka na musamman
 6. Zainab Gummi - Ma’aikatar ilimi.
 7. Sufyan Yuguda - Ma’aikatar kudi
 8. Fa’eka Marshal - Ma’aikatar harkokin jin kai da annoba
 9. Rabiu Gusau - Ma’aikatar ayyuka da tafiye-tafiye
 10. Yazeed Fulani - Ma’aikatar sana’o’i da ma’aikatu
 11. Ibrahim Gusau - Ma’aikatar dazuka da bunkasa kiwon dabbobi
 12. Nuradden Gusau - Ma’aikatar ma’adanai
 13. Junaidu Kaira - Ma’aikatar shari’a
 14. Akwai Ibrahim Magayaki - Ma’aikatar noma
 15. Ibrahim Dosara - Ma’aikatar labarai
 16. Yahaya Gora - Ma’aikatar ilimin gaba da sakandare
 17. Yahaya Kanoma - Ma’aikatar samar da ayyuka da bunkasa arziki
 18. Lawal Badarawa - Ma’aikatar bunkasa al’umma
 19. Sheikh Jangebe - Ma’aikatar harkokin addini
 20. Aliyu Tukur - Ma’aikatar kasafi da tsari,
 21. Aliyu Tsafe - Ma’aikatar lafiya,
 22. Mamman Tsafe - Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida,
 23. Abubakar Tsafe - Ma’aikatar yawon bude ido da kula da otal
 24. Ibrahim Mayana - Ma’aikatar ruwa
 25. Abubakar Bore - Ma’aikatar bunkasa kauyaku.

Source: Legit

Online view pixel