Shugabancin APC: Jerin Sunayen yan takarar da suka yi fatali da umarnin Buhari, suka mika Fam Hedkwata

Shugabancin APC: Jerin Sunayen yan takarar da suka yi fatali da umarnin Buhari, suka mika Fam Hedkwata

  • Yayin da ranar 26 ga watan Maris da APC zaɓa don gudanar da babban taronta ke ƙara natsowa, yan takara na cigaba da cike sharudda
  • Duk da wasu bayanai sun nuna shugaba Buhari ya nuna zabinsa, amma har yanzun wasu yan takara ba su hakura ba
  • A cewarsu maganar da ake cewa shugaba Buhari ya faɗa ba gaskiya bane, domin kakakinsa ya fitar da sanarwa

Abuja - Masu hankoron kujerar shugaban APC na ƙasa sun soma miƙa Fom ɗin sha'awar takara a Sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa dake Abuja, yayin da babban taro ke kara matsowa.

Majiyoyi daga cikin APC sun shaida wa Daily Trust yadda shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya goyi bayan Sanata Abdullahi Adamu a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

Adamu da Al-Makura
Shugabancin APC: Jerin Sunayen yan takarar da suka yi fatali da umarnin Buhari, suka mika Fam Hedkwata Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce:

"A wani taro, shugaban ƙasa ya faɗa mana shugaban jam'iyya ya fito daga arewa ta tsakiya kuma wanda yake so shi ne Sanata Abdullahi Adamu. Ba wanda ya masa musu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma duk da haka, sauran yan takara dake hankoron kujerar shugaban jam'iyya, sun yi kunnen uwar shegu, sun ƙi janye kudirinsu.

Wasu yan takaran sun yi takakka da kansu wajen miƙa Fam bayan sun cike, wasu kuma sun maida Fam ɗin ta hanyar tura wakilai.

Jerin waɗan da suka maida Fom

Waɗan da suka miƙa Fom bayan cikewa sun haɗa da, Sanata mai wakiltar Neja ta gabas, Sanata Sani Musa; tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura; da tsohon gwamnan Benuwai kuma Ministan ayyuka na musamman, George Akume.

Sauran yan takatar da suka maida Fom dinsu bayan cikewa sune tsohon Mataimakin shugaban CPC da ta rushe, Saliu Mustapha, tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu da Mohammed Saidu Etsu.

Kara karanta wannan

'Zan cika burin yan Najeriya' Matashi dan shekara 45 ya shiga tseren gaje kujerar Buhari a 2023

Babu wanda ya faɗa mana an yi sulhu - Sanata Musa

Yayin hira da manema labarai jim kaɗan bayan maida Fom, Sanata Musa ya ce jam'iyya ba ta sanar da su cewa an yi sulhu kan kujerar shugaban jam'iyya ba.

Da aka tambaye shi, Sanata Musa ya ce:

"Meyasa jam'iyya zata siyar mana da Fom? Iya abun da nasani shi ne ba bu wanda ya tuntuɓe ni a hukumance ko wani ɗan takara."
"Kuma kamar yadda kakakin shugaban ƙasa ya faɗa, babu wanda Buhari ya nuna masa goyon baya."

A wani labarin kuma Kungiya a arewa ta lale miliyoyi ta siyawa Atiku Abubakar Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a 2023

Kungiyar yan kasuwan arewa maso gabas sun lale miliyoyi sun karban wa Atiku Abubakar Fom ɗin sha'awar tsayawa takara a PDP.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna tsantsar farin cikinsa tare da godiya gare su bisa wannan karamci.

Kara karanta wannan

Kungiya a arewa ta lale miliyoyi ta siyawa Atiku Abubakar Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel