2023: Wata Kungiya a Arewa a saya wa Atiku Abubakar Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a PDP

2023: Wata Kungiya a Arewa a saya wa Atiku Abubakar Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a PDP

  • Kungiyar yan kasuwan arewa maso gabas sun lale miliyoyi sun karban wa Atiku Abubakar Fom ɗin sha'awar tsayawa takara a PDP
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna tsantsar farin cikinsa tare da godiya gare su bisa wannan karamci
  • A jawabinsa ya bayyana yadda wasu matasa suka kafa tarihi a zaɓen 2019, wajen saya masa Fom

Awanni 24 bayan jam'iyyar hamayya PDP ta buɗe siyan Fom ɗin takara a zaben 2023, kungiyar yan kasuwan arewa maso gabas ta ta saya wa Atiku Abubakar.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan Fom ɗin takara ya zo hannunsa, Atiku, ya bayyana yadda wasu matasa suka kafa tarihi a Najeriya a 2019, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Fom ɗin takara
2023: Wata Kungiya a Arewa a saya wa Atiku Abubakar Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a PDP Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce:

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun tattara maza da mata 47

"A 2018 ko 2019 za'a ce wasu matasa sun haɗa kuɗi kuma suka saya mun Fom na takara, karo na farko a tarihin siyasar Najeriya tun bayan dawowar demokaraɗiyya."
"Suka tattara kuɗaɗen da suka nema da gumin su kuma suka karɓo min Fom, wannan abu ya sa na zubda hawaye, na shiga shauki."
"Yanzu kuma kamar yadda kuka ji daga bakin shugaban ƙungiya, an gayyace mu kuma aka mun wani karamci, duk da alƙawari ne, amma ga shi yau an cika shi."

Ban taba ganin wannan yanayin ba tun da nike - Atiku

Atiku ya ƙara da cewa kalubalen da yan Najeriya ke kwana su ta shi da shi ya girmama, "ban taba ganin irin wannan kalubalen ba a tarihin kasar nan."

Kara karanta wannan

Mafarauci ya bindige tsohon shugaban APC har Lahira, ya ce ya ɗauka wata dabba ce

"Haɗin kan mu ya yi rauni, tattalin arzikin mu ya shiga mataki mafi muni tun da muka samu yanci a matsayin ƙasa. Tsaron mu kuma sai lahaula, kalubale dai sun mamaye mu ta ko ina."
"Mutum ɗaya, ko tawagar ɗai-ɗaikun mutane ba za su iya warware waɗan nan kalubalen ba. Amma suna bukatar taimakon kowa. Dan haka yan uwa maza da mata, yan Najeriya abin da ke gaban mu ba karami bane."

A wani labarin kuma Batanci ga Annabi: Kotun Musulunci a Kano Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Sheikh Abduljabbar

Babbar Kotun Musulunci a Kano dake sauraron karar Abduljabbar ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar ba da beli.

Alkalin Kotun ya sanya ranar 31 ga watan Maris, 2022 domin bayyana matsayar Kotu kan bukatar bayan sauraron ɓangarorin biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel