Yadda Jarumar Finafinan Najeriya Ta Kamu da Cuta Mai Hatsari a wajen Ɗaukar Fim
- Jaruma Omowunmi Dada ta kamu da cutar sepsis yayin daukar fim a Oyo, kuma masu fim din sun bar ta a otal ba tare da kulawa ba
- Jrumar ta ce masu shirya fim din sun nemi ta biya su cikon kudin aikin da ba ta karasa ba, ba tare da damuwa da rashin lafiyarta ba
- A zantawarmu da jarumi Abdul M Shareef, sh
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Omowunmi Dada, wata fitacciyar jarumar Nollywood ta bayyana cewa ta kamu da cuta mai hatsari ta sepsis yayin da take daukar shirin fim a garin Oyo.
Rahoto ya nuna cewa sepsis wata cuta ce da ke da hadari ga rayuwar mutum wadda take karya garkuwar jiki da tsayar da aikin kayan ciki.

Asali: Twitter
Bayanin jaruma Dada na zuwa ne yayin da kawarta, Jemima Osunde ta ba da lamarin yadda ta kamu da cutar H. pylori a wajen daukar fim, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan
Jirgin Max Air da ya tashi daga Legas zuwa Kano ya yi hatsari, an samu karin bayani
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaruma Osunde ta ce ta kamu da cutar H. pylori wadda ake samunta daga cin abinci mai guba a lokacin da taje daukar fim a Ibadan, birnin jihar Oyo.
Yadda jaruma ta kamu da cutar sepsis
Osunde ta ce ta shafe shekaru uku tana fama da wannan cutar wadda har ta rikide ta koma cutar gastroesophageal reflux (GERD).
Da take magana game da labarin da Osunde ta bayar, jaruma Dada ta ba da nata labarin na yadda ta kamu da cutar sepsis a wajen shirin fim a Oyo.
Jarumar ta ce masu shirya fim din sun watsar da ita a otel, har sai da iyayenta da tawagarta suka shirya yadda aka kai ta wani asibiti a Ibadan.
Dada ta ce daga baya kuma masu shirya fim din suka nemi ta biya su kudin fim din da suka tura mata tunda dai ba ta yi aikin ba.
A shafinta na X, jaruma Osunde ta yi martani ga wannan lamari da ya faru da Dada, inda ta yiwa Ubangiji godiya da ya sa abokiyar sana'arta ta rayu.
Wata jaruma ta kamu da cutar H.Pylori
Ita ma ta ba ta labarin yadda masu shirya fim suka nemi ta biya kudin da aka tura mata alhalin a wajen daukar shirinsu ne ta kamu da cutar H.Pylori.
Osunde ta ce:
"Kin kamu da Sepsis? Mun godewa Ubangiji da ya ba ki lafiya 'yar uwa. Ni ma haka na kai kai na asibitin Legas, na biya kudin magani, amma suka zo suna neman na biya su kudin aiki.
"Lokacin da tawagata ta aika masu da rahoton ka'idojin da suka karya na aikin da zan yi masu, sai suka yi shiru. Wai suna neman na biya su kudi alhali ko sannu ba su yi mun ba."
Abdul M Shareef ya yi tsagewar kashi a Bauchi
A zantawarmu da fitaccen jarumin Kannywood, Abdul M Shareef kan irin kalubalen da jarumai ke fuskanta a wajen daukar fim, ya ce ya taba tsagewar kashi a Bauchi.
Abdul M Shareef ya shaidawa wakilin Legit Hausa, Sani Hamza Funtua cewa:
"Za ka iya tunawa lokacin da muka je wani aiki a Bauchi, na samu tsagewar kashi. Dole na hakura na dawo gida na warke kafin na koma aka karasa aikin.
Da Sani ya so jin abin da ya faru, Abdul ya ce:
"Wani 'scene' ne ake dauka na fada. To an hada ni fada da wasu garada, irin masu cin karfen nan, da wani ana ce masa Dalma, da marigayi Shola Army.
"Mun yi kokawa, mun yi dambe mun yi fada, har ta kai shi Dalma ya daga ni sama ya kada ni, to ashe tun a nan kashi na na hannun dama ya tsage.
"Mun ci gaba da daukar aikin, sai hannun ya fara amsawa, na fara jin ciwo. Wasa wasa dai harba na iya daga hannun, sai da aka mayar da ni gari aka kama mun."
Abdul ya ce ya sa kamuwa da rashin lafiya a wajen daukar fim, to amma ya dauki hakan a matsayin wani bangare na neman halaliyarsa.
'Yan damfara sun yashe Mansura Isah
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohuwar jarumar Kannywood ta koka yayin da ta ce 'yan damfara sun yi kutse a asusun bankunanta sun sace mata kudi.
Mansura Isah ta nuna takaici yadda 'yan damfarar suka yashe asusunta tatas tare da mayar da ita talakar karfi da yaji yayin da kuma ta caccaki bankunanta.
Asali: Legit.ng