An Caku Tsakanin 'Yan Mata 2 da Kowacce ta Hadawa Saurayi 1 Bazday, Sun ci Karo a Gidansa

An Caku Tsakanin 'Yan Mata 2 da Kowacce ta Hadawa Saurayi 1 Bazday, Sun ci Karo a Gidansa

  • Wata budurwa ta labarta yadda ta so ba saurayin ta mamaki ranar zagayowar haihuwarsa ta hanya kawo masa kyautuka da dauko masa masu busa algaita
  • Ga mamakinta, ta iske wata budurwa a gidansa tana shirya masa sha tara ta arizki, wanda hakan ya janyo suka ba hammata iska
  • Hakan ya yi sanadin samun raunin daya daga cikin masu busa sarewar, inda daga bisani biyun suka gane yaudararsu ya ke

Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Juwon ta labarta yadda aka ba hammata iska ranar zagayowar haihuwar saurayinta yayin da ta iske shi tare da wata budurwa.

Mata Biyu
An Caku Tsakanin 'Yan Mata 2 da Kowacce ta Hadawa Saurayi 1 Bazday, Sun ci Karo a Gidansa. Hoto daga lailanews.com
Asali: UGC

Budurwar mai shekaru 21 ta bayyana yadda ta shirya wa saurayin nata bikin zagayowar ranar haihuwarsa a matsayin ba-zata inda ta yi hayar mai busa algaita da kyautuka, ga mamakinta ta iske wata budurwa a gidan shi tana shirya mishi irin abun da ta shirya.

Kara karanta wannan

Kin Tsufa Da Haihuwa: Matashiya Ta Fashe Da Kuka Wiwi Lokacin Da Ta Ji Mahaifiyarta Na Da Cikin ‘Da Na 5

Take a nan 'yan matan suka kwashi dambe a gidansa, wanda ya yi sanadiyyar samun raunin daya daga cikin masu busa algaitar da suka zo da su.

Abun mamaki shi ne yadda suka gano babu wacce yake so da gaske a cikin su biyun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Juwon:

"Na bukaci mai busa algaita ya taimaka min don ba saurayi na mamaki ranar zagayowar haihuwarsa. Ni da wata yarinya muka je tare da wasu daban don bashi mamaki.
"Hakan ya yi sanadiyyar samun raunin daya daga cikin masu busa sarewar. Daga karshe dai mu biyun mun gano yaudararmu yake."
Juwon
An Caku Tsakanin 'Yan Mata 2 da Kowacce ta Hadawa Saurayi 1 Bazday, Sun ci Karo a Gidansa. Hoto daga lailanews.com
Asali: UGC

Ma'aikaciya ta tsinta makuden kudi, ta mayar da su ga masu shi

A wani labari na daban, wata ma'aikaciya da ta kwashe shekara tana zuwa aiki a kasa ta tsinta kudin da suka kai kimar N6.908 miliyan a kasa yayin da ta ke dawowa daga aiki.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Zasu iya Zuwa: Bayanai 4 Game da Kwalejin Berea a Amurka Wacce ke Karbar dalibai Kyauta Har da Abinci

Daga ganin kudin ta nufi caji ofis da su inda aka nemo masu kudin. Ashe wasu ma'aurata ne aka basu matsayin gudumawa na aurensu amma suka yadda.

Tuni 'yan sandan suka kafa gidauniyar taimakon matar wacce za a hada mata kudin da za ta siya motar kanta da shi.

A halin yanzu an hada mata kudin da suka kai $25,000 daga cikin $45,000 da ake fatan hadawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel