Karatu Kyauta: Abubuwa 4 Muhimman Game da Kwalejin Amurka da ke Karbar 'Yan Najeriya, har da Abinci Kyauta

Karatu Kyauta: Abubuwa 4 Muhimman Game da Kwalejin Amurka da ke Karbar 'Yan Najeriya, har da Abinci Kyauta

  • Wata makaranta a Amurka, kwalejin Berea, su na bada karatu kyauta ga duk dalibansu ko da ba mazauna US bane
  • Kwalejin Berea d na bukatar dalibai su mika kebantattun bayani tare da rubuce-rubucensu da takardun amincewa
  • 'Yan Najeriya da suka kalli bidiyon game da makarantar sun nuna sha'awar shigar da bukata yayin da suke tambayar matakan da suka dace

Yayin da 'yan Najeriya ke neman damar shillawa kasar waje, wasu bidiyon TikTok da YouTube sun bayyana yadda wata makaranta, Kwalejin Berea, inda ba a bukatar dalibai su biya kudin makaranta.

Makaranta a US
Karatu Kyauta: Abubuwa 4 Muhimman Game da Kwalejin Amurka da ke Karbar 'Yan Najeriya, har da Abinci Kyauta. Hoto daga Berea College
Asali: Getty Images

Legit.ng ta duba shafin yanar gizon makarantar inda ta gano yadda ta dauki tsawon lokaci tana aiki ba tare da biyan ko ficika ba tun 1892, kuma daliban kasar waje za su iya shigar da bukata tare da yin maraba da su.

Kara karanta wannan

Tsadar Mai Da Naira: A Tausayawa Talaka, a Tausaya Wa Al'umma: Gwamnan Bauchi ga Gwamnatin Tarayya

Nenye, wacce ta yi ikirarin ta yi makarantar ta ce kuma tana samar ma dalibai aiki yayin da suke karatu. Ta kara da cewa ana bada abinci kyauta.

Ga wasu abubuwa hudu da ya kamata 'yan Najeriya su sani yayin shigar da bukatarsu kwalejin Berea:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Mihimman ranakun shigar da bukata

Shafin yanar gizon kwalejin ta sanar da cewa tana bada damar shigar da bukatar shiga duk shekara ranar 15 ga watan Oktoba ba kamar yadda aka saba ba a watan Janairu. Sanarwa ga wadanda suka hanzarta shigar da bukatarsu na zuwa a tsakiyan Disamba

2. Kwafi uku na takardar makarantar sakandirin ka

Kwalejin Berea ta ce tarihin dole ya kasance a Yaren Turanci. Haka zalika, tarihin ya zama daga hukumar makaranta. Wadanda suka kunsa sakamakon jarabawa kamar WAEC.

3. Sai rubutun zube da mai shigar da bukata zai yi

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hadimar Gwamna Tambuwal Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto

Duk wani dalibi daga kasar waje da zai shiga Berea dole ya mallaki rubutun zube da ba zai gaza tsakanin shafi biyu zuwa uku ba, kuma babu wani dalili da mai shigar da bukata zai nemi agaji yayin tsara rubutun.

4. Makin jarabawarsa kwarewa a Turanci

Kwalejin ta bada zabi ga daliban kasashen ketare da ko dai su gabatar da SAT, TOEFL, IELTS, ACT ko Duolingo. Duk wani 'dan Najeriya da ke da ra'ayi zai iya duba shafin yanar gizonsu don samun wasu bayanai game da makarantar.

Martanin 'yan soshiyal midiya

Ga wasu daga cikin martanin 'yan soshiyal midiya game da kudin makarantar kwalejin kyauta.

Joel MUNYANEZA ta yi tambaya:

"Nima kwalejin Berea za ta ki amsata saboda na rubuta berea a matsayin barea a rubutun zube na, da kuma malamai na amincewa."

Bushemere Shillah ta yi tambaya:

"Ko akwai shekarun da idan mutum ya kai ba za a amsa bukatarsa ba? Kuma ga wanda ya gama karatu shekaru biyar da suka wuce amma bai je jami'a ba za su iya shigar da bukatarsu?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel