Kin Wuci Daukar Ciki: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Da Ta Ji Mahaifiyarta Za Ta Sake Haihuwa

Kin Wuci Daukar Ciki: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Da Ta Ji Mahaifiyarta Za Ta Sake Haihuwa

  • Wata budurwa ta bayyana damuwarta lokacin da ta ji cewa mahaifiyarta na da cikin da na biyar
  • A wani bidiyo da ya yadu, matashiyar wacce ke ganin mahaifiyar tata ta tsufa da haihuwa ta kasance da hawaye a idanunta
  • Daga cikin wadanda suka yi martani kan bidiyon akwai mutanen da suka fahimci damuwarta a matsayinta na yar fari

Wata matashiya yar shekaru 13 ta kadu matuka da jin labarin cewa mahaifiyarta na dauke da cikin 'da na biyar. Ta bayyana zuciyarta a wani bidiyo da ya yadu.

Dauke da hawaye a idanunta, matashiyar budurwar ta fada ma mahaifiyar tata cewa ta tsufa da daukar juna biyu kuma cewa bai kamata mahaifinta ya dunga yi wa mutane ciki ba a wannan shekaru nasa.

Ya da iyayenta
Kin Tsufa Da Daukar Ciki: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Da Ta Ji Mahaifiyarta Za Ta Sake Haihuwa Hoto: TikTok/@itz_shayb4
Asali: UGC

Yadda ta dauki abun da muhimmanci a dan gajeren bidiyon ya haddasa martani masu yawan gaske yayin da mutane suka ce tana hango yadda za ta sha zaman raino ne.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Duk da 'ya'ya 5 da Muke da su, Mijina ya Koma Tarayya da Yayata, Yayi watsi da ni da 'Ya'yana, Matar Aure

Akwai mutanen da suka bayyana cewa sun fahimci radadinta a matsayinta na yar fari wacce aikinta zai karu da sabon jinjiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Sparqlyy ta ce:

"Ta san cewa babu makawa za ta sha zaman raino."

This_is_Kay ta ce:

"A matsayinta na 'yar fari, na fahimci damuwarta."

Kayla ta ce:

"Tana nuna damuwarta sannan su suna dariya."

The_Chocolate_Unicorn ta ce:

"Ta gaji da aikin zaman raino ban ga laifinta ba."

Jai ta ce:

"A'a gaskiya na fahimceta saboda kasancewarmu yan fari mune uwa na biyu...kuma idan duk kuka tafi sune damuwrmu."

Uwa ta samo dan mutum-mutumi tana nuna masa gata tunda ta gaza samun jika

A wani labari na daban, wata uwa ta dauki mataki ta hanyar samo mutum-mutumi tana kula da shi tare da nuna masa gata saboda diyarta mai shekaru 21 ta ki haifa mata jika.

Diyar matar wacce ta nadi bidiyon mahaifiyar tata tana shirya yaron ta cika da mamakin wannan al'amari inda ta ce har yanzu ita din yarinya ce karama kuma ko saurayi bata da shi balle har a kai ga batun samun ciki da haihuwar jikkale.

Asali: Legit.ng

Online view pixel