Budurwa ta Tunkari Mahaifiyarta Bayan Ta Gano Cewa Ba a Titi aka Samo Cikinta

Budurwa ta Tunkari Mahaifiyarta Bayan Ta Gano Cewa Ba a Titi aka Samo Cikinta

  • Wata budurwa cike da mamaki ta gano cewa mutumin da ya raine ta tun tana karama a matsayin 'diyarsa ba shi bane mahaifinta na asali
  • Budurwar mai suna Lane ta wallafa bidiyo a dandalin TikTok tare da bayyana yadda ta gano asalin mahaifinta bayan samun sakonnin waya da dama daga wanda bata sani ba
  • Masu amfani da kafar sada zumuntar TikTok sun sha mamaki bayan ganin bidiyon, wanda daya daga ciki yayi yawo wanda sama da mutane 10 miliyan suka duba

Wani gwajin kwayar halitta yayi sanadin da wata budurwa ta gano cewa mutumin da ta kwashe tsawon rayuwarta tana kira mahaifinta ba shi bane asalin mahaifinta.

Burdurwa
Budurwa ta Tunkari Mahaifiyarta Bayan Ta Gano Cewa Ba a Titi aka Samo Cikinta. Hoto daga TikTok/@laneiscool14.
Asali: UGC

A wasu jerin bidiyo da ta wallafa a TikTok, budurwar mai suna Lane ta bayyana yadda ta samu sakonnin waya daban-daban daga wani mutum da bata san ko waye ba, wanda ya bukaci tayi gwajin kwayoyin halittarta.

Kara karanta wannan

Maa Ta Nadi Bidiyon Mijinta Yana Shan Wankin Kayanta, An Yi Cece-kuce

Budurwa bata yi kasa a guiwa ba, hakan yasa ta gano cewa mutumin da take dauka matsayin mahaifi ba shi bane ya haifeta.

Hakan ya tabbatar mata da cewa mahaifiyarta ta ci amanar mahaifinta. Lane ta fuskanci mahaifiyarta wacce ta bayyana mata cewa yayin da take jami'a, ta ci amanar mijinta, wanda hakan ne ya jawo har ta dauki ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lane ce sakamakon wannan cikin, inda hakan ya zama sirri tun lokacin. Mutumin da ya dirka mata cikin ya san Lane 'diyarsa ce, sannan yana ta kokarin yadda zai kulla alaka da ita.

Lane ta wallafa hotunan sabon mahaifinta bayan gwajin kwayar halittar da tayi gami da gano gaskiya cike da mamaki, hakan yasa tace a yanzu mahaifa biyu gareta. Ta fadi hakan ne tare da bayyana mamakinta:

"Sai da na kusa faduwa daga kujerata. Tayi ci amana da wani wanda taba shekaru 10 lokacin da take jami'a. Hakan ya faru ne sau daya, amma da ya ganta a makaranta ya ce, wannan nawa ne? amma ta musanta.”

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Garzayo Najeriya Daga Turai Domin Haduwa Da Sahibinta, Bidiyonsu Ya Yadu

"Daga baya na gano cewa wannan mutumin shine mahaifina. Hakan yasa na tura masa sakon kar ta kwana, yanzu haka yana zaune a California. Bature ne."

Martanin jama'a

@rose4856 ta ce:

"Hala a take kika gano harshenki na turai? Wasa nake. Amma hakan da mamaki. Da yanzu rayuwarki ta canza gaba daya."

#it's a Sonderful Life ya ce:

"Tana jami'a amma ta bashi shekaru 10."

@Ashhhh ya ce:

"Kaga mutumi. Yana kaunarki daga nesa na tsawon lokaci. Amma abun da burgewa da ya riga ya san ko ke wacece."

@lilmilenial yayi martani:

"Ina zubda hawaye hakan da ban takaici da ya jira tsawon wannan lokaci."

Magidanci ya gane yara 5 da matarsa ta haifa ba nashi bane

A wani labari na daban, wani magidanci ya gane cewa yara 5 da matarsa ta haifa ba nashi bane.

Gwajin kwayar halitta na DNA ya nuna cewa babban ‘dansu mai shekaru 32 har zuwa karamin mai shekaru 15 ba nashi bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel