Buhari Ya Dauki Muhimmin Mataki Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU

Buhari Ya Dauki Muhimmin Mataki Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU

  • A halin yanzu al'umma sun sa ido suna kalon yadda Shugaba Muhammadu Buhari zai warware yajin aikin kungiyar ASUU
  • Kamar yadda wasu yan Najeriya da dama ke tsammani, musamman yan jami'a, shugaban kasar ya kira taro mai muhimmanci a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba
  • Mashawarci na musamman ga shugaban kasa, Bashir Ahmed, ya bayyana cewa wasu jagororin jami'o'in tarayya sun halarci taron

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga wani taro da wasu mambobin kwamitin jagororin jami'o'in tarayya a Najeriya.

A cewar daya daga cikin hadiman shugaban kasa, Bashir Ahmad, ana taron ne a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari
Buhari Ya Dauki Muhimmin Mataki Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU. Hoto: Aso Rock Villa.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ahmaad ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 16 ga watan Satumba.

"Shugaba Muhammadu Buhari, a yanzu yana ganawa da wasu zababbun mambobin kwamitin jagororin jami'o'in tarayya, a gidan gwamnati da ke Abuja."

Duk da cewa ba a san abin da za a tattauna a wannan taron ba, ana kyautata zaton taron sirrin ba zai rasa nasaba da yunkurin Buhari na kawo karshen yajin aikin ASUU da ya ki ci ya ki cinyewa ba.

Yayin taron, Buhari ya sha alwashin sake tuntuba masu ruwa da tsaki da suka dace, domin kawo karshen yajin aikin da ya-ki-ci-ya- ki cinyewa.

Kalamansa:

"Zan sake tuntuba, sannan in sanar da ku abin da ake ciki. A matsayin na shugaban kasa kuma babban kwamandan hafsoshin kasa, kuma mai ziyara zuwa jami'o'in tarayya."

Shugaban kasar, ya cigaba da cewa, "abubuwan alheri za su faru a jami'o'in kasar nan gaba."

Ya janyo hankalin kan yadda jami'ar Ibadan ta samu shiga cikin jami'o'i 1,000 da ke kan gaba a duniya.

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi ya ce ilimin Jami'a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.

Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.

Asali: Legit.ng

Online view pixel