Kotu Ta Tura Shaharren Mawaki Ice Prince Zamani Gidan Yarin Ikoyi

Kotu Ta Tura Shaharren Mawaki Ice Prince Zamani Gidan Yarin Ikoyi

  • Kotu ta bada umurnin a tura mawakin gambara na Najeriya, Panshak Zamani wanda aka fi sani da Ice Prince zamani gidan gyran hali
  • Hakan na zuwa ne bayan kama shi da yan sanda suka yi kan dukkan dan sanda da barazanar jefa shi a rafi lokacin da aka tare shi yana tuki babbu lamba
  • Alkalin kotun, amma, ya bada belin mawakin kan kudi N500,000 da mutum biyu tsayayyu da za su karbe shi idan ya cika sharrudan

Legas - An tsare fitaccen mawakin gambara na Najeriya, Panshak Zamani wanda aka fi sani da Ice Prince Zamani a gidan yarin Ikoyi.

Benjamin Hundeyin, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Legas, ya shaidawa Premium Times cewa an gurfanar da mawakin a kotun majistare da ke Ajah a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

2023: An Sake Zargin Peter Obi Da Wani Babban Abu Da Zai Iya Janyo Masa Matsala A Takarar Shugaban Kasa

Ice Prince
Kotu Ta Tura Mawaki Ice Prince Zamani Gidan Yarin Ikoyi. Hoto: @Benhundeyin.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An gurfanar da shi kan tuhume-tuhume uku masu alaka da duka, sace mutum da hana hukuma aikinta.

Dukkan Dan Sanda

Hundeyin, cikin sanarwar da ya fitar a Twitter ya ce an kama mawakin.

Ya ce an kama Ice Prince ne kan dukkan dan sanda da ya tsare shi saboda yana tuki ba tare da lamba ba a motar.

A sakon da ya wallafa a Twitter, Mista Hundeyin ya ce mawakin ya yi barazanar zai jefa dan sandan a cikin rafi a lokacin da aka kama shi.

Dan sandan ya wallafa hoton mawakin da ankwa a hannunsa yana mai cewa za a gurfanar da shi a kotu.

Beli

Mr Hundeyin ya shaidawa Premium Times cewa an bada belin wanda ake zargin kan sharuddan biyan N500,000 tare da masu tsaya masu guda biyu.

Kara karanta wannan

Akan N1,500 na kudin wutan lantarki, wani ya bindige kaninsa har lahira

Ya kara da cewa za a saki mawaki da zarar ya cika sharrudan belin.

An dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Satumba.

Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Umurci Mawaki Portable Ya Kai Kansa Ofishinta Ko Ta Kamo Shi

A wani rahoton, Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Ogun ta umurci fitaccen mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya kai kansa ofishinsu mafi kusa nan take ko kuma a kama shi.

Hakan ya biyo bayan zargin duka da aka ce ya yi wa tsohon DJ dinsa mai suna DJ Chicken, rahoton Daily Trust.

A wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Portable, wanda ya yi magana da harshen Yarbanci ya umurci yaransa su yi wa DJ Chicken duka kan zargin ya tura wa matarsa sako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel