"Ina Dalili": Gumi Ya Nemi Majalisa Ta Duba Yawan Kashe Fararen Hula da Sojoji ke Yi
- Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya buƙaci Majalisar Dattawa ta shiga batun yawan kai hare-hare da sojoji kan fararen hula
- Ya ce ta’aziyya kaɗai ba ta wadatar ba, ganin yadda yanzu lamarin kai hari bisa kuskure ke neman zama ruwan dare a wasu daga cikin jihohin Najeriya
- Rahotanni sun ce wani sabon hari da sojojin suka kai bisa kuskure kan wata kasuwa da ke iyakar Borno da Yobe ya kashe mutum 200
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bukaci Majalisar Dattawa ta duba batun hare-haren jiragen sojin sama da ake zargin sun kashe fararen hula a wasu sassan Najeriya.
Gumi ya bayyana hakan ne bayan harin sojoji ta sama ya kashe fararen hula kusan 200 a kasuwar Jilli da ke da iyaka da jihohim Borno da Yobe.

Source: Facebook
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu , 2026, Sheikh Gumi ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da irin wadannan hare-hare.
Sheikh Ahmad Gumi na neman a tuhumi sojoji
Jaridar Punch ta wallafa cewa Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana mamaki a kan yadda matuka jiragen ke ki hari a kan bayin Allah da ba su yi laifin komai ba.
Ya ce:
“Su waye matukan jiragen da ke sakin bama-bamai a kan fararen hula da ba su yi laifin komai ba?”
Ya kuma tuno wasu wurare da irin wadannan hare-hare suka taba faruwa, ciki har da Tudun Biri, Nasarawa, Sokoto da sauran yankuna.
Gumi ya yi Allah wadai da hare-haren sojoji
Sheikh Gumi ya jaddada cewa irin wadannan hare-hare da ake kira kuskure sun jawo asarar rayuka masu yawa a baya, musamman harin Tudun Biri da ya faru a watan Disambar 2023 a jihar Kaduna.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Ba za a iya yaki da ta’addanci da wani irin ta’addanci ba. Dole ne a gaggauta gudanar da zaman sauraron ra’ayi a Majalisar Dattawa kan wadannan hare-hare da ake kira kuskure da ake kai wa kauyuka, kasuwanni da fararen hula. Muna bukatar amsa, ba wai ta’aziyya kawai ba.”
Sai dai gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce kasuwar Jilli da ke karamar hukumar Gubio an rufe ta tun shekaru biyar da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Dauda Iliya, ya fitar, gwamnan ya bayyana yankin a matsayin wurin da ake zargin mayakan Boko Haram da masu kai masu kayayyaki ke amfani da shi.
Gwamnan Borno ya goyi bayan sojoji
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi cikakken bayani game da kasuwar da sojojin sama suka jefa wa bama-bamai a ƙarshen mako.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: An shiga firgici da aka gano gawarwakin mutane sama da 60 a jihar Neja
A cewar Farfesa Zulum, an riga an rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka wuce saboda an gano ta zama dandalin ƴan ta'adda, inda suke saye da sayarwa.
Gwamnan ya goyi bayan aikin sojojin tare da gargaɗin mazauna jihar Borno a kan mu'amala da ƴan ta'adda saboda kare rayukansu, tare da neman su bada haɗin kai.
Asali: Legit.ng

