Wata Sabuwa: Jami'an Tsaro Sun Dira a Gidan Abubakar Malami, an Ji Abin da Ya Faru
- Jami'an tsaro sun kai samame a gidan tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami a babban birnin tarayya Abuja
- Abubakar Malami bai dade da samun beli ba a kararrakin da hukumomin EFCC da DSS suka shigar a kansa
- Tsohon Ministan ya nuna rashin gamsuwarsa kan abin da ya kawo jami'an tsaron zuwa gidansa inda ya fito ya kalubalance su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jami’an tsaro sun kai samame gidan tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami.
Abubakar Malami SAN, wanda ya kasance a tsare bisa zargin karkatar da kuɗaɗe, kwanan nan aka ba shi belin sa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa jami'an tsaron sun kai samamen ne a gidan Abubakar Malami a ranar Litinin, 23 ga watan Maris 2026.
Jiga-jigan ADC na ziyartar Abubakar Malami
Manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, sun ziyarce shi a gidansa tun bayan da ya samu ’yanci.
Sai dai kuma, sa’o’i kaɗan bayan Atiku ya bar gidan, jami’an tsaro sun far wa gidan na Malami.
Yadda ta kaya tsakanin Malami da jami'an tsaro
A cikin wani bidiyo da @KafinHausaa ya sanya a shafin X, an ji Malami, wanda har a lokacin yake sanye da irin tufafin da ya tarbi Atiku da su yana cewa:
“Nuna mani inda aka ce ku zo ku ƙwace gida na. Yayin da lamarin yake gaban kotu, shin kuna da ikon yin wani abu na musamman?”
Wani jami'i sanye da kayan gida ya ba shi amsa da cewa:
“Muna da haƙƙin yi wa gida alama muddin gidan yana ƙarƙashin ikon ƙwacewa."
Abubakar Malami ya kalubalanci jami'an tsaron da cewa:
“Shin yana ƙarƙashin ƙwacewa ne alhalin lokacin umarnin ya ƙare? Umarnin da aka bayar na kwanaki 14 ya ƙare sannan kun zo don ku kunyata ni. Tun da sanyin safiya kuka je ɗayan gidan nawa sannan yanzu kuna nan. Ina umarnin da ya ba ku izinin zuwa gidana ku yi masa alama? Umarnin nake son gani.”

Kara karanta wannan
Rabon shinkafar Tinubu: Yadda ake 'bambance' Kudu da Arewa wajen tallafa wa mutane

Source: Twitter
Wani jami'in tsaro ya ba shi amsa da cewa:
“Wannan shi ne umarnin; na ba ka umarnin, yallaɓai."
Tsohon Ministan ya sha alwashin cewa zai kalubalanci abin da aka yi masa a gaban kotu.
"Ina takardar umarnin kotu da kuke da ita na yi wa gida na alama? Kuna ƙoƙarin kunyata ni ne ko mene ne? Umarnin da ke nan ba takamaimai ba ne, ta fuskar doka ba ku damar yi wa gida na alama. Duk da haka, kuna iya ci gaba da yin hakan. Za mu haɗu a kotu.”
- Abubakar Malami
Kotu ta umarci a tsare Abubakar Malami
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin tsare tsohon Antoni Janar Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a gidan gyaran hali na Kuje.
Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta aika da Malami tare da matarsa, Hajia Bashir Asabe, da dansu, Abubakar Abdulaziz Malami, zuwa gidajen yari.
Kotun ta ki amincewa da rokon belin da aka yi ta baki, inda ta bukaci lauyoyinsu su shigar da takarda a hukumance duba da nauyin zargin da ake musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
