ICPC Ta Sanya Lokacin Gurfanar da El Rufai gaban Kotu bayan Kwashe Dogon Lokaci a Tsare
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shirya gurfanar da Malam Nasir Ahmad El-Rufai a gaban kotu
- ICPC ta sanar da tuhume-tuhumen da take yi wa tsohon gwamnan na jihar Kaduna bayan ya dade tsare a hannunta
- Hukumar ta bayyana cewa za ta gurfanar da Nasir El-Rufai ne a ranar Talata, 24 ga watan Maris 2026
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ICPC ta sanar da lokacin da za ta gurfanar da Nasir Ahmad El-Rufai a gaban kotu.
Hukumar ICPC ta bayyana cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan na jihar Kaduna a gaban kotu a ranar Talata, 24 ga watan Maris 2026.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ICPC, John Okor Odey, ya sanya a shafin X na hukumar a ranar Litinin, 23 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan
"Yan ta'adda na amfani da bidiyon azabtarwa don firgita al’umma": Masani ya bayar da mafita
Nasir El-Rufai ya dade a tsare
El-Rufa’i ya kasance a tsare tun bayan da ya amsa gayyatar hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2026.
Hukumar EFCC ta gudanar da bincike a kansa na tsawon sa’o’i 48 kafin daga bisani hukumar ICPC ta mayar da shi ƙarƙashin kulawarta.
Tsawaita tsare El-Rufa’i ya haifar da fushin jama’a, inda ƙungiyoyi da daidaikun mutane da dama suka yi kira ga hukumar da ta gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma ta sake shi.
Wane tuhume-tuhume ICPC ke yi wa El-Rufai?
A cikin sanarwar da ya fitar, kakakin na hukumar ICPC ya ce za a gurfanar da El-Rufa’i a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Talata.
“Karar mai lamba FHC/KD/73/2026 tana ɗauke da tuhume-tuhume da suka haɗa da sauyawa da mallakar dukiyar gwamnati da kuma karkatar da kuɗaɗe."
“Haka zalika, an shigar da wata tuhumar, mai lamba KDH/KAD/ICPC/01/26, a kan Malam Nasir El-Rufa’i da wani mai suna Amadu Sule (LEDA), a gaban babbar kotun jihar Kaduna."

Kara karanta wannan
Ana cikin murnar Sallah, Iran ta shammaci Amurka da Isra'ila a sababbin hare hare
“Tuhume-tuhumen da ke cikin shari’ar babbar kotun jihar sun haɗa da cin zarafin ofis, zamba, da niyyar aikata zamba da ba wa kai ko wani fifikon da bai dace ba, da sauran su."
“Hukumar ICPC ce ta shigar da dukkan tuhume-tuhumen a ranar 18 ga watan Maris, 2026."
“Za a sanar da ranar gurfanarwa a babbar kotun jihar a lokacin da ya dace kamar yadda kotun ta amince.”
- John Okor Odey

Source: Facebook
Hukumar ICPC ta bayyana cewa an riga an mika wa El-Rufa’i takardun sammaci kamar yadda doka ta tanada.
El-Rufai ya yi nasara a kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun daukaka kara da ke zamanta a Kaduna ta soke hukuncin da kotun tarayya ta yanke a wata kara da tsohon gwamna, Nasir El-Rufai, ya shigar a kan majalisar dokokin jihar.
A hukuncin da kotun ta yanke, ta bayyana cewa an samu kura-kurai a shari’ar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuli, 2024.
Kotun daukaka karar ta ayyana hukuncin a matsayin maras tushe tare da umartar a mayar da shari’ar zuwa kotun tarayya domin a sake ba wa wani alkalin daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng