Ana Rade Radin Kafa Sansanin Sojin Amurka a Najeriya, Dakarun Kasar Sun Yi Bayani
- Rundunar tsaron Najeriya ta yi karin bayani game da yarjejeniyar da ta kulla da dakarun Amurka da yanzu haka suke wasu yankuna na kasar
- A kwanakin baya an yada rade-radi game da ayyukan da sojojin Amurka za su yi a Najeriya tare da bukatar a fito da yarjejeniyar fili kowa ya ganta
- A yunkurin sanar da 'yan kasa hakikanin abin da ke faruwa, Manjo Janar SM Uba ya yi bayani kan rade-radin kafa sansanin sojin Amurka a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yayin wata tattaunawa, daraktan yada labaran hedikwatar tsaro, Manjo Janar SM Uba, ya bayyana ainihin yanayin dangantakar soja tsakanin rundunar sojin Najeriya da rundunar sojin Amurka.
Hakan na zuwa ne bayan yada rade-radin cewa Amurka na son kafa sansanin soji a Najeriya bayan shigowarsu kasar da sunan kare Kiristoci.

Source: Facebook
Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ya wallafa abubuwan da rundunar sojin Najeriya ta fada game da alakar da ta kulla da kasar Amurka a shafinsa na X.
Amurka za ta yi sansani a Najeriya?
Manjo Janar Uba ya bayyana cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Amurka ba ta nufin kafa sansanin sojin Amurka a Najeriya ba ne.
Ya ce wannan haɗin gwiwa ta ta’allaka ne kacokan kan haɗin kan sojin kasashe biyu wanda ya fi karkata ga horaswa, ƙarfafa dakarun Najeriya, da musayar bayanan sirri domin ƙarfafa tsaron kasa.
A cewarsa, irin wannan haɗin gwiwa ba ta takaitu ga Amurka kaɗai ba, ya ce Najeriya tana da irin wannan haɗin gwiwar tsaro da wasu ƙasashe da dama.
Ya ce Najeriya na hakan ne a matsayin wani ɓangare na babban shirin ta na inganta ƙwarewar soja da kuma ƙarfafa ikon ta wajen tunkarar ƙalubalen tsaro.
A cewarsa:
"An tsara waɗannan shirye-shiryen ne domin taimaka wa rundunar sojin Najeriya ta rungumi kyawawan hanyoyin aiki na duniya tare da inganta aikinta wajen kare kasa."
Kasar Amurka za ta mutunta Najeriya
Manjo Janar Uba ya jaddada cewa duk wata haɗin gwiwar soja ta ƙasa da ƙasa da ta shafi Najeriya ana gudanar da ita ne tare da cikakken mutunta iko da kuma muradun ƙasa.
Mahalarta tattaunawar sun amince cewa a yanayin tsaro na duniya a yau, inda ƙasashe ke da alaƙa da juna sosai, dole ne haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe domin magance barazanar tsaro masu rikitarwa.

Source: Facebook
The Nation ta wallafa cewa sun kuma bayyana cewa irin waɗannan haɗin gwiwa na taimakawa rundunar soja, matukar za a tabbatar da cewa Najeriya na ci gaba da riƙe cikakken ikonta.
Amurka ta rufe ofis a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa ofishin jakadancin Amurka ya dakatar da aiki a birnin tarayya Abuja saboda barazanar barkewar zanga-zanga.

Kara karanta wannan
Bayan rantsar da shi, shugaban 'yan sandan Najeriya ya tabo batun yakin Iran da Amurka
Ofishin ya sanar da ranar da zai fito aiki idan abubuwa sun lafa, inda ya bukaci wadanda ya yi wa alkawari da su duba sakon da ya tura musu ta imel.
Ana fargabar 'yan Shi'a za su yi zanga-zanga a Abuja ne domin nuna bacin rai game da harin Amurka/Isra'ila da ya kashe Ayatollah Khamenei.
Asali: Legit.ng

