Jingir Ya Yi Fito na Fito da Shirin Kafa ’Yan Sandan Jihohi, Malamin Ya Yi Zargin Munafurci
- Shugaba majalisar malamai na kungiyar Izala reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nuna adawa da shirin kafa ‘yan sandan jihohi
- Sheikh Jingir ya yi gargadin akwai yiwuwar amfani da su don murkushe abokan adawa a Plateau wanda ba zai zama da dadi ba
- Malamin ya roki Bola Ahmed Tinubu da ya yi taka-tsantsan kafin amincewa da tsarin ‘yan sandan jihohi a fadin kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya shiga muhawarar da ake yi kan kafa ‘yan sandan jihohi da ake ganin zai magance matsalolin tsaro.
Shugaban malaman kungiyar Izala reshen Jos ya bayyana fargabarsa kan yiwuwar amfani da tsarin wajen murkushe abokan hamayyar siyasa a jihar Plateau.

Source: Facebook
'Yan sandan jihohi: Sani Jingir ya yi gargadi
Jingir ya ce bai dace a bai wa jihohi ikon kafa rundunar ‘yan sanda ba tare da tsauraran matakan kariya daga cin zarafi ba, kamar yadda Zagazola Makama ta ruwaito.
A cikin wani bidiyo, Jingir ya bayyana cewa a yanayi mai cike da rabuwar kawuna ta siyasa da addini kamar Plateau, rundunar tsaro ta jiha na iya zama makamin siyasa.
Ya yi wata magana da ke nuna zargin tsohon gwamna a jihar Plateau da cewa yana da hannu a tashe-tashen hankula da aka yi a mulkinsa.
Ya ce:
“Ku fada mana, lokacin da yake kan mulki, wa ya wadata? Berom nawa ya kashe? Fulani nawa ya kashe? Hausawa da Kiristoci nawa ya kashe? Har ma ana zargin cewa yana da hannu a cire koda na wasu makusantansa.”
Malamin ya bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya yi taka-tsantsan kafin amincewa da shirin ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa dole ne a kafa tsare-tsare masu karfi don hana amfani da su ba bisa ka’ida ba.
Ya ce wasu ‘yan siyasa na iya fakewa da kafa rundunar domin far wa wadanda ba su goyi bayan akidarsu ba wanda hakan zai jawo matsala mai grma.

Source: Facebook
Rikicin Plateau: Jingir ya wanke Gwamna Caleb
Jingir ya kuma yi ishara da zargin cewa wani tsohon gwamnan jihar na iya kokarin tayar da zaune tsaye domin amfanin siyasa, ko da yake bai gabatar da hujjoji kai tsaye ba.
Sai dai ya wanke gwamnan Plateau na yanzu, Caleb Mutfwang, da hannu a rikice-rikicen da ake fuskanta, yana mai cewa bai ga alamar cewa gwamnan yana da hannu a lamarin ba.
A karshe, malamin ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da hadin kai a Plateau, tare da kira ga Musulmi da Kiristoci da su fifita tattaunawa da mutunta juna domin kauce wa sabbin rikice-rikice.
Sheikh Jingir ya dura kan shugaban INEC
A baya, mun ba ku labarin cewa Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya ce naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban INEC babban haɗari ne.
Sheikh Jingir, wanda shi ne Shugaban majalisar malaman JIBWIS ya ce Musulman Najeriya ba su aminta da nadin Amupitan ba saboda wasu dalilai da suke ganin bai dace da kujerar ba.
Dattijon malamin addinin ya bukaci Majalisar Tarayya ta sa baki domin tabbatar da adalci da amincewar jama’a gabanin zaben 2027da ake tunkara.
Asali: Legit.ng

