Gwamnan Zamfara Ya Saye Jiragen Yaki domin Gamawa da 'Yan Bindiga

Gwamnan Zamfara Ya Saye Jiragen Yaki domin Gamawa da 'Yan Bindiga

  • Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya saye kayan yaki da suka hada da jirage marasa matuka domin tallafawa dakarun Najeriya
  • Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya) ya halarci taron kaddamar da kayan yakin, inda ya yaba wa gwamna Dauda Lawal
  • Christopher Musa ya yaba wa gwamnan bisa abubuwan cigaba da ya ce ya gani an kawo Zamfara yana mai cewa jihar tana kan turba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamafara - Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yaba wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa sayo motocin sulke, jiragen leƙen asiri marasa matuƙa, da sauran kayan yaki ga jami’an tsaro.

Gwamnan ya miƙa motoci masu sulke da sauran kayan aiki ga dakarun tsaro a wani biki da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gusau.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna Zulum ya ware Musulmi da Kiristoci 300,000, ya raba tallafin azumi

Yadda aka kaddamar da jirgin yaki a Zamfara
Jirgin yaki da aka kaddamar a Zamfara. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

An saye jiragen yaki a Zamfara

A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Facebook, motocin sulke 25 da aka ƙaddamar za su ƙara kare jami’an tsaro yayin da suke shiga yankunan da ke da haɗari a faɗin jihar Zamfara.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa sauran kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta saya sun haɗa da jiragen leƙen asiri marasa matuƙa.

An bayanna cewa jiragen na da ƙarfin tashi na tsawon mita 80, wanda zai iya tafiyar nisan kilomita 50 tare da aiki na tsawon awa takwas ba tare da tsayawa ba.

Bayanin gwamnan Zamfara a taron

Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, gwamna Lawal ya ce halartar ministan tsaro a taron na nuna ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta Zamfara.

Rahoton Radio Nigeria ya nuna cewa ya ce:

“Tsawon shekaru, jihar Zamfara ta fuskanci matsalar tsaro. Yankunan karkara sun fuskanci rashin kwanciyar hankali, manoma sun shiga cikin rashin tabbas, kuma zirga-zirga a manyan hanyoyi ta kasance cikin tsoro.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan mutane da suka ziyarci kasuwar Singer bayan mummunar gobara

"Kasuwanni sun yi rauni, rashin tsaro ya shafi yawan amfanin gona, kuɗin shiga da zaman lafiya. Waɗannan matsaloli sun shafi rayuwar yau da kullum da tattalin arziki."
Motocin yaki da aka saya a Zamfara
Motocin yaki da aka kaddamar a Zamfara. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

“Asusun tallafawa tsaro na jihar Zamfara ya samar da tsayayyen tsari na tallafin kayan aiki ga jami’an tsaro. Mun ƙarfafa haɗin kai da rundunar sojoji, ’yan sanda da sauran hukumomi.
“A matsayin mu na gwamnati, ba ma yin ƙasa a gwiwa wajen samar da duk abin da jami’an tsaronmu ke buƙata."

Bayanin ministan tsaron Najeriya

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce sayo motoci masu sulke da gwamnatin Zamfara ta yi na nuna jajircewar gwamnan.

Ya ce:

“Daga abin da na gani, idan muka ci gaba da haka a wa’adi na biyu, Zamfara za ta zama kamar Dubai."

Tambayar da ake kan sojojin Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan Najeriya ana tambayoyi game da zuwan sojojin Amurka Najeriya da sauke su a jihar Bauchi.

Lauya mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Audu Bulama Bukarti ya bukaci karin bayani kan dalilin ajiye sojojin a Bauchi maimakon wasu jihohi.

Bulama ya bayyana cewa Bauchi akwai wasu jihohin Najeriya da suka fi bukatar jami'an tsaro domin suna fama da matsalolin tsaro sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng