Mutanen da Aka Sace Suna tsakiyar Ibada a Kaduna Sun Bar Hannun 'Yan Bindiga

Mutanen da Aka Sace Suna tsakiyar Ibada a Kaduna Sun Bar Hannun 'Yan Bindiga

  • Wasu kiristoci da 'yan bindiga suka sace daga coci guda uku a garin Kurmin Wali a jihar Kaduna sun shaki iskar 'yanci
  • Rahotanni sun nuna cewa an sako mutanen a daren jiya Laraba kuma ana tsammanin an wuce da su gidan gwamnatin Kaduna
  • Har yanzu babu tabbacin an biya kudin fansa ko an kai wa 'yan bindigar baburan da suka bukata tun farko kafin su saki mutanen

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - An sako kiristocin da aka yi garkuwa da su suna tsakiyar ibada a coci a garin Kurmin Wali da ke yankin Kufana a ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Rahotanni sun tabbatar da cewa masu ibadar sun bar hannun 'yan bindiga, sun shaki iskar 'yanci bayan shafe makonni da dama a hannun masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Bayan jiran kusan shekaru 50, Uba Sani ya kaddamar da hanya a kauyukan Kaduna

Kurmin Wali.
Cocin ECWA da ke garin Kurmin Wali a karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna Hoto: Ayuba John
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an sace waɗannan mutane ne a ranar 18 ga watan Janairun 2026, sa’ilin da suke gudanar da ibada a cikin garin ranar Lahadi.

Yadda mutanen suka kubuta daga masu garkuwa

Wani jagoran al'umma wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an sako mutanen ne a daren jiya Laraba.

Ya bayyana cewa tsakanin ƙarfe 11:00 na dare zuwa tsakar dare, an ga manyan motoci suna shiga cikin daji a kusa da garin Maro, sannan daga baya suka dawo tare da mutanen da aka sace tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na dare.

"Ba mu san su wane ne suka je ɗauko su ba kuma ba mu san wurin wa aka karbo su ba. Haka nan, ba mu da tabbacin ko dukkaninsu ne aka sako, amma dai an tabbatar da sakin nasu," in ji shi.

Kara karanta wannan

'Mutane sun yi ta kansu,' Halin da ake ciki a garin da aka kashe sojan Najeriya

Shin an biya 'yan bindiga kudin fansa?

Har yanzu ba a tabbatar da ko an biya kuɗin fansa ba, ko kuma an ba wa masu garkuwar babura 17 da suka nema a baya kafin su sako mutanen ba.

Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 177 ne aka sace a lokacin harin na Kurmin Wali. Kimanin makonni biyu bayan sace su, mutane 80 (mafi yawansu yara) sun samu nasarar tserewa daga hannun 'yan ta'addan.

Magajin Gari ya yaba wa gwamnatin Kaduna

Mai garin Kurmin Wali, Ishaku Dan’azumi, ya tabbatar da wannan labari, inda ya gode wa gwamnatin jihar Kaduna da jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suka yi na ganin mutanen sun dawo lafiya.

Kara karanta wannan

Harin Kwara ya kara muni, adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya haura 80

Ya ƙara da cewa waɗanda aka sako sun haɗa da yara, mata, da manya, sai dai bai bayar da takamaiman adadinsu ba.

Gwamna Uba Sani.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani a gidan gwamnati Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Duk da cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto gwamnatin Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, bayanai cewa an wuce da mutanen zuwa gidan gwamnati jihar domin tantance su da kuma duba lafiyarsu.

An sace 'yan kasuwa 4 a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun tare wasu sanannun yan kasuwa hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, sun yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

Wata majiya da ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Juma’a sa’ilin da mutanen ke dawowa daga kasuwar Maro.

'Yan bindigan sun yi wa 'yan kasuwar kwanton bauna a hanyar Maro zuwa Kajuru, suka tattara su suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262