Abu Ya Girma: Gwamnati Ta Bada Umarnin Rufe Makarantu a fadin Jihar Kogi

Abu Ya Girma: Gwamnati Ta Bada Umarnin Rufe Makarantu a fadin Jihar Kogi

  • Gwamnatin Kogi ta sanar da rufe dukkan makarantun jihar biyo bayan wasu rahotanni sirri da ta samu da suka shafi tsaron cikin gida
  • Gwamnati ta bayyana cewa matakin rufe makarantun na rigakafi ne domin kare dalibai da malamai daga fadawa hannun 'yan ta'adda
  • Gwamna Ahmed Ododo ya umurci jami'an tsaro da su gaggauta dakile duk wata matsalar tsaro don dalibai sun koma karatu cikin aminci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - A ranar Talata, 3 ga Fabrairu, 2026, gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da rufe dukkan makarantu na firamare da sakandare na jihar nan take.

Wannan mataki ya biyo bayan umarnin gaggawa da gwamnati ta bayar domin kiyaye rayukan ɗalibai da malamai a jihar.

Gwamnatin Kogi ta bada umarnin rufe dukkan makarantu a fadin jihar.
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo zaune a ofishinsa da ke Lokoja. Hoto: @OfficialOAU
Source: Facebook

An rufe makarantu a jihar Kogi

Shugaban ƙungiyar masu makarantun kuɗi (NAPPS) na jihar, Pastor Reuben Jimoh, ya tabbatar wa mambobinsa wannan umarni, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

An biyo kan masu shara: Gwamna ya yi barazanar korarsu kan rijistar zama yan APC

A cikin saƙon gaggawa da ya aika wa masu makarantu, Pastor Jimoh ya bayyana cewa wannan umarni ya shafi kowa.

Ya ce:

“An matso da hutun tsakiyar zango sabanin yadda aka tsara shi, yanzu za a rufe makarantu har zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu, 2026.”

Jimoh ya jaddada cewa:

“Babu makaranta daga gobe har zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu. Kada wata makaranta ta ƙetare wannan umarni.”

Wannan mataki ya jefa iyaye da ɗalibai cikin rudani, amma gwamnati ta ce hakan ya zama dole domin kare rayukan dalibai da malamai.

Dalilin rufe makarantun jihar Kogi

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin rigakafin abin da ka iya faruwa.

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin gwamnatin Kogi na intanet, Fanwo ya bayyana cewa gwamnati ta samu sahihan rahotannin sirri dake nuna bukatar ƙarfafa tsaro a makarantun jihar baki ɗaya.

A cewarsa, Gwamna Ahmed Usman Ododo ya ba da umarnin ɗaukar matakan gaggawa domin tabbatar da cewa an koma karatu cikin sauri.

Kara karanta wannan

Jira ya kare: NECO ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare, SSCE 2025

An umarci makarantu su rufe a Kogi har zuwa ranar 16 ga Fabrairu, 2026.
Wani bangare na makarantar sakandaren mata ta Dapchi da ke jihar Yobe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haɗin gwiwa da jami'an tsaro

Gwamnatin jihar ta yaba wa jami'an tsaro kan yadda suke bayar da rahotannin sirri akan lokaci domin dakile dukkan wata barazana ta tsaro.

Fanwo ya ƙara da cewa:

“Jami'an tsaro suna aiki dare da rana domin gano inda maboyar miyagun mutane take domin murƙushe su.”

Ya ba wa mazauna jihar tabbacin cewa gwamnati tana nan daram wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya a kowane yanki.

Wannan shi ne karon farko da gwamnatin Ododo ta ɗauki irin wannan ƙataccen mataki tun bayan hawansa mulki a jihar Kogi.

Rundunar 'yan sandan jihar ta kuma tabbatar da tura ƙarin dakarun sintiri zuwa yankunan manyan makarantun kwana, musamman wadanda suke a karkara.

An rufe dukkan makarantu a Ebonyi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantu a wasu yankuna a jihar.

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne a yankin Amasiri da ke Karamar Hukumar Afikpo, tare da sanya dokar hana fita ta awanni 20 a kullum.

A zantawarsa da 'yan jarida, gwamnan ya bayyana jerin matakan tsaro da na gudanarwa domin dawo da zaman lafiya da hana sake faruwar irin wannan hari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com