'Yan Sanda Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Raga Raga yayin Artabu a Kaduna

'Yan Sanda Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Raga Raga yayin Artabu a Kaduna

  • Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun yi dauki ba dadi da wasu tsagerun 'yan bindiga masu dauke da makamai a jihar Kaduna
  • 'Yan bindigan sun ji ba dadi ne yayin da suka yi yunkurin kai hari kan wani kauye saboda gaza biyan kudin harajin da aka kakaba musu
  • Kwamishinan 'yan sandan Kaduna ya yaba kan nasarar da jami'an suka samu tare da ba da tabbacin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Rundunar ’yan sanda ta jihar Kaduna ta ce ta yi nasarar dakile wani hari da ’yan bindiga suka kai a karamar hukumar Giwa.

Rundunar 'yan sandan ta ce jami'anta sun samu nasarar hallaka mutane biyu daga cikin ’yan bindigan are da kwato makamai daga hannunsu.

'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga a Kaduna
Sufeto Janar na rundunar 'yan sanda, Kayode Egbetokun da jami'an 'yan sanda na fareti Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fasa kofa, an ga gawarwarin mutum 6 da suka kwanta barci

An yi galaba kan 'yan bindiga a Kaduna

Rundunar ta bayyana cewa aikin ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da aka samu na cewa ’yan bindiga na shirin kai hari kauyen Idisu, da ke gundumar Idisu a yankin Bayan Kogi.

Kakakin 'yan sandan ya ce bayanan sirrin sun nuna cewa ’yan bindigan, karkashin jagorancin wani shahararren jagoransu, Kachalla Sanusi Bajira, na shirin mamaye yankin, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da hakan.

Ya ce 'yan bindigan sun yi shirin mamaye yankin ne bayan da mazauna kauyen suka gaza biyan harajin dole da aka kakaba musu ba bisa ka’ida ba.

'Yan sanda sun fafata da 'yan bindiga

DSP Mansir Hassan ya ce bayan samun bayanan, kwamishinan ’yan sanda ya ba da umarnin a tura jami’an sashen yaki da sace-sace, tare da hadin gwiwar ’yan Civilian Joint Task Force (CJTF), zuwa yankin da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki amarya da wasu 'yan gidan biki, an rasa rayukan bayin Allah

Da isarsu, jami’an tsaro sun gamu da ’yan bindigan da suka yi kwanton bauna, inda nan take aka shiga musayar wuta tsakaninsu.

Sai dai jami’an tsaron sun yi nasarar rinjayar ’yan bindigan, inda aka hallaka biyu daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin dazuzzuka na kusa.

A yayin aikin, an kwato bindigogi biyu da harsasai guda biyar.

'Yan sanda sun yi artabu da 'yan bindiga a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinan 'yan sanda ya yabawa jami'ansa

A nasa bangaren, kwamishinan ’yan sanda, Rabiu Muhammad, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin bisa jarumtaka da kwarewa.

Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar za ta ci gaba da ayyukan tsaro bisa bayanan sirri domin yaki da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran manyan laifuffuka.

Ya kuma gargadi masu aikata laifi da cewa jihar Kaduna ba za ta zama mafakar mutane marasa gaskiya ba.

'Yan bindiga sun farmaki amarya

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan bayin Allah a Katsina.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tura wasiku ga al'umma da Turanci, za su kai hari saboda haraji

‘Yan bindiga ne sun kai hari kan tawagar biki a Unguwar Nagunda, Karamar Hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Tsagsrun sun yi awon gaba da bakin da suka halarci biki da dama, kuma har yanzu ba a san adadinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng